Labaran Kannywood: Mahaifiyata ta ce duk wanda ya sake zagina na rama ba ta yafe mini ba - Adam Zango
A wata hira da manema labarai suka yi da fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan wato Adam A Zango, ya bayyana cewa ya yi matukar mamaki kuma yaji kunya sosai da har Ali Nuhu, wanda ya dauka a matsayin abin koyi, yaya a masana'antarsu ya kai shi kara kotu
Ga yadda hirar ta su ta kaya da manema labarai:
Yaya ka ji a lokacin da aka ce Ali Nuhu ya kai karar ka kotu?
Da sammaci ya zo mini, ni da kai na na tura masa sako na ce wallahi ka ba ni kunya matuka, ni da nake ganin cewa ina da dangi sama da mutane dari biyar, amma da na haifi dana na farko ban saka sunan kowa ba sai naka, ai ko darajar wannan karamcin dana yi maka bai kamata ka yi min abinda kayi ba. Ballantana zagi, zagin ma bana bidiyo ba, zagi ne guda daya.
Dangantakarku ta yi tsamin da ba za a iya sulhunta ku ba kenan?
Ai maganar sulhu ta riga ta kare an riga an sulhunta mu na kuma ba shi hakuri. Kawai dai abin da na ke so abokanan aikina da kuma duniya su gane shi ne, an ce mutunci madara ne, idan ya bare, ba za ka iya kwashewa ba. Saboda haka, rana mai kamar ta yau lokacin da nayi hira da ku, da ace wani yaron Ali zai shiga shafukan sada zumunta, ya zagi uwata ya zagi ubana ya zagi duka dangina, ya fadi duk abin da ya ga dama, ba zan taba kula shi ba har abada. Saboda mahaifiyata ta ce mun, "idan wani ya kara zagina" ko da kuwa ita ya zaga, idan na maida masa martani, ba ta yafe mini ba.
KU KARANTA: Rayuwar wata al'umma a Najeriya da ba a taba kawo musu wutar lantarki ba
A makonnin da suka gabata ne fitaccen jarumin Adam Zango ya sanya wani sako a shafinsa, inda ya yi ikirarin cewa tun da har Ali Nuhu ya sa aka ciwa mahaifiyarsa mutunci, shi ma sai ya rama.
Daga baya Ali Nuhu ya kai Adamu Zango kotu, inda har kotu ta aika wa da Zango sammaci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana
Asali: Legit.ng