Rayuwar wata al'umma a Najeriya da ba a taba kawo musu wutar lantarki ba

Rayuwar wata al'umma a Najeriya da ba a taba kawo musu wutar lantarki ba

- Ko kun san akwai wani tsibiri a cikin jihar Legas da tunda aka kirkire shi ba su taba ganin wutar lantarki ba

- Manema labarai sun yi hira da wasu daga cikin mazauna garin, inda suka nuna rashin jin dadin su akan irin rayuwar da suke yi ba tare da wutar lantarki ba

Wani bincike da aka gabatar ya nu na cewa akwai wani gari a Najeriya da tunda aka kirkire shi basu taba samun wutar lantarki ba.

A wata hira da manema labarai suka yi da mazauna garin, sun nuna rashin jin dadin su matuka da irin halin da suke ciki. Ga yadda hirar ta kaya da wani mai suna Joseph Tamilade Damola.

"Ba mu samun wuta kwata-kwata haka muke zama kullum, ba Ikoyi ba ne ko Lekki, wannan wani tsibiri ne shima daban, sunan shi Tsibirin Sabokoji.

Rayuwar wata al'umma a Najeriya da ba a taba kawo musu wutar lantarki ba

Rayuwar wata al'umma a Najeriya da ba a taba kawo musu wutar lantarki ba
Source: Facebook

"Wani abin mamaki shine, daga inda muke muna iya ganin tashar jirgin ruwan Najeriya. Amma ba mu da wuta, muna cajin wayoyin mu a kan kudi naira 50. Duk da babu wuta haka muke rayuwa, muna kallon wasan kwallon kafa a kan kudi naira 100," in ji shi.

Haka ita ma wata mata da aka yi magana da ita bayyana yadda rayuwarta ta koma bayan dawowarta tsibirin.

KU KARANTA: Kano: Wani mutumi ya yiwa wata budurwa yankan rago saboda ta ki bashi hadin

"Bayan gwamnati ta rushe gidana da ke Tsibirin Tincan, sai na dawi nan na nemi gida akan kudi naira 20,000. Bayan na samu gidan a nan, sai gobara ta auku inda ta kone komai nawa, nima dakyar mutane suka ceto rayuwata.

"Ina amfani da itace wurin dafa abinci, haka nan da wutar muke kwana a daki domin samun haske, duk kuwa da irin matsanancin zafin da muke ji," in ji matar.

"A lokacin Fashola an taba gina mana burtsate, da ya lalace sai Mai Garin nan ya dauke ba mu san ina ya kai ba, amma tun lokacin ba mu kara ganinta ba," in ji Damola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel