An kama wadanda suka yi garkuwa da surukar gwamnan Katsina

An kama wadanda suka yi garkuwa da surukar gwamnan Katsina

Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina ta shelanta cewar ta kama wadanda ake zargi da sace mahaifiyar matar gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, tare da yin garkuwa da ita a cikin watan Maris.

Da yake tabbatar da kama mutanen, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce sun mika wadanda suka kama zuwa hedikwatar 'yan sanda dake Abuja domin cigaba da bincike a kan su.

A cewar sa: "da gaske ne mun kama mutane da dama dake da hannu a kan lamarin kuma mun mika su zuwa hedikwatar mu ta Abuja domin cigaba da gudanar da bincike a kan su."

Wasu mutane sun sace mahaifiyar Hajiya Binta, matar gwamna Masari a cikin watan Maris, sannan sun sake ta bayan wasu 'yan kwanaki kalilan.

An kama wadanda suka yi garkuwa da surukar gwamnan Katsina

'Yan sandan Najeriya
Source: Twitter

Dattijuwar, Hajiya Maisitiyari, da aka sace, na da shekaru 80 a duniya.

DUBA WANNAN: 'So ake a bata maka suna saboda kai mutumin kirki ne' - Majalisa ta wanke Emefiele daga zargin badakala

Kazalika, kakakin ya bayyana cewar har yanzu rundunar 'yan sanda na cigaba da bincike a kan garkuwa da Alhaji Musa Umar, Magajin garin Daura kuma suruki ga babban dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sannan ya kara da cewa rundunar 'yan sanda na aiki tukuru, ba dare ba rana, domin tabbatar da cewar ya dawo gida ga iyalinsa cikin koshin lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel