Gwamna Ganduje ya ba Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar kyautar Naira miliyan uku-uku

Gwamna Ganduje ya ba Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar kyautar Naira miliyan uku-uku

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da kyautar Naira Miliyan ga kowane daya daga cikin Mutane biyu da hukumar kasar Saudiyya ta sallamo daga gidan kurkuku bayan kuskuren kama su da laifin fataucin miyagun kwayoyi.

Tsuntsu daga sama gasasshe ya riski Zainab Aliyu da kuma Ibrahim Abubakar, yayin da gwamnan Kano Ganduje da ake yiwa lakabi da Khadimul Islama ya ba kowanen su kyautar Naira Miliyan uku-uku domin rangwanta masu radadi na halin kunci da suka fuskanta yayin kasancewar su a gidan 'Dan Kande a kasa mai tsarki.

Gwamna Ganduje yayin jawaban bayar da kyautar N3m ga Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar

Gwamna Ganduje yayin jawaban bayar da kyautar N3m ga Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar
Source: Facebook

Gwamna Ganduje ya ba Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar kyautar miliyan uku-uku

Gwamna Ganduje ya ba Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar kyautar miliyan uku-uku
Source: Facebook

Gwamna Ganduje yayin bayar da kyautar N3m ga Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar

Gwamna Ganduje yayin bayar da kyautar N3m ga Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar
Source: Facebook

Yayin jawaban godiya a fadar gwamnatin Kano

Yayin jawaban godiya a fadar gwamnatin Kano
Source: Facebook

Zainab Aliyu yayin jawaban godiya a fadar gwamnatin Kano

Zainab Aliyu yayin jawaban godiya a fadar gwamnatin Kano
Source: Facebook

Kusoshin gwamnatin Kano yayin shaidar ba Zainab da Ibrahim kyautar kudi

Kusoshin gwamnatin Kano yayin shaidar ba Zainab da Ibrahim kyautar kudi
Source: Facebook

Gwamna Ganduje ya mika godiyar sa ta musamman ga dukkanin wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen ganin Zainab da kuma Ibrahim sun samu 'yanci kama daga shugaban cibiyar kula da harkokin kasashen ketare, Honarabul Abike Dabire da kuma Iyayen Zainab.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar AAC ta nemi a cafke gwamnan bankin Najeriya

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jakadan kasar Saudiya zuwa Najeriya, Adnan Mahmoud Bostaji, yayin taron buda bakin azumi da aka gudanar aranar Talata cikin ofishin jakadancin kasar Saudiya da ke Najeriya a garin Abuja, ya ce tuni ya ayyanawa ran sa cewa Zainab da Ibrahim za su samu 'yanci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel