Abinda yasa ragowar kabilun Najeriya basu fahimci 'yan kabilar Igbo ba - Rochas
- Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce ragowar kabilun Najeriya basu fahimci 'yan kabilar Igbo ba
- Okorocha ya bayyana cewar kabilar Igbo ce aka fi yiwa mummunar fahimta a Najerya
- Gwamnan ya bayyana cewar ana tsangwamar 'yan kabilar Igbo a duk inda suka je a fadin kkasar nan, kamar ba 'yan Najeriya ba
Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya ce ragowar kabilun Najeriya sun yiwa 'yan kabilar mummunar fahimta.
Okorocha ya bayyana cewar babu wata kabila a Najeriya da aka yiwa mummunar fahimta kamar kabilar Igbo.
Jaridar Vanguard ta rawaito Rochas na cewa burin dan kabilar Igbo a duk inda ya samu kan sa shine ya taimaki rayuwar mutanen da yake rayuwa tare da su.
Gwamnan ya kara da cewa amma abin takaicin shine yadda ragowar kabilun Najeriya ke daukan wannan halin kirki na 'yan kabilar Igbo a matsayin rauni.
Okorocha na wadannan kalamai ne a wurin taron manyan sarakunan kasar nan da aka yi a jihar Imo domin tattauna batun son balle wa daga Najeriya da mazauna yankin arewa maso gabas ke yi.
Ya shaida wa sarakunan cewar akwai alheri a cikin cigaban zaman yankin a cikin Najeriya.
A cewar sa: "a matsayin na dan kabilar Igbo, na yi imani da zaman Najeriya a matsayin kasa daya mai al'umma daban-daban. Na tashi ne a yankin arewa, sannan na koyi neman kudi a yankin kudu maso yamma. Ina da hujjar yarda da Najeriya.
DUBA WANNAN: Kotu ta rushe sabbin masarautu da sarakunan da Ganduje ya nada
"Ina son yin amfani da wannan damar domin yin kira ga 'yan Najeriya da su rungumi akidar nuna kauna ga dukkan 'yan kasa domin ta hanyar yin hakan ne kadai za a samu hadin kai da fahimtar juna. Hakan ne kadai za sa mu kalli dukkan matsalar dake damun wani yanki a matsayin matsalar kasa baki daya, ba matsalar yakin da abin ya shafa ba.
"Dan kabilar Igbo ne kadai zai je wani yanki na Najeriya ya raya wurin, wasu ma basa dawowa mahaifar su. Amma wasu 'yan Najeriya na daukan wannan hali na 'yan kabilar a matsayin rauni. Hakan ne kuma ya sa a duk yanki da 'yan kabilar suke ake korar su kamar ba 'yan Najeriya ba," a cewar Rochas.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng