Da dumi-dumi: Dakarun NAF sun kashe 'yan bindiga 12, sun kubutar da mutane 15 a dajin Kaduna

Da dumi-dumi: Dakarun NAF sun kashe 'yan bindiga 12, sun kubutar da mutane 15 a dajin Kaduna

Rundunar soji sama tace aikinta na Operation DIRAN MIKIYA da take na da hadin gwiwa da dakarun sojojin reshe na 271 tayi nasarar kashe yan fashi da makami 12 a dajin Kamuku, Birnin Gwari, Kaduna.

A cewar rundunar sojin saman, jami’anta sun kuma taimaka wajen sakin mutum 15 da aka yi garkuwa da su.

Air Commodore Ibikunle Daramola, jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a raar Talata, 14 ga watan Mayu a Abuja.

A kwanan nan ne rundunar ta kaddamar da aikin jami’anta na 271 a Birnin Gwari, jihar Kaduna, a duk daga cikin kokarin magance matsalolin tsaro a kasar.

Da dumi-dumi: Dakarun NAF sun kashe 'yan bindiga 12, sun kubutar da mutane 15 a dajin Kaduna

Da dumi-dumi: Dakarun NAF sun kashe 'yan bindiga 12, sun kubutar da mutane 15 a dajin Kaduna
Source: Facebook

Daramola yace kafa rudunar sojin sama ta 271 a Birnin Gwari na haifar da yaya masu idanu.

A cewarsa wannan aiki da rundunar ta kaddamar a yankin yayi sanadiyar halaka yan bindiga 12 da kuma ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su.

KU KARANTA KUMA: Zababbun sanatoci 5 na zawarcin kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa (jerin sunaye)

Kakakin rundunar ya ba yan Najeriya tabbacin cewa rundunar sojin sama za ta ci gaba da aiki da rundunar tsaro na sama da sauran hukumomin tsaro domin dorar da aikinta na fatattakar yan bindiga daga yankin arewa maso yamma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel