Zaben Majalisa: ‘Dan Majalisar APC Gbajabiamila ya samu goyon baya mai rinjaye

Zaben Majalisa: ‘Dan Majalisar APC Gbajabiamila ya samu goyon baya mai rinjaye

Mun samu labari cewa Honarabul Femi Gbajabiamila yana cigaban da samun goyon bayan ‘yanuwansa da ke majalisar tarayya wajen samun nasarar lashe zaben majalisar wakilai da za ayi.

A farkon Watan gobe ne za a zabi sababbin shugabanni a majalisar Najeriya, wanda Femi Gbajabiamila yake ganin cewa ya lashe zaben majalisar wakilai ya gama, ganin irin gagarumin goyon bayan da yake samu kawo yanzu.

Honarabul Femi Gbajabiamila wanda shi ne ‘dan takarar da jam’iyyar APC mai mulki ta tsaida a zaben na bana ya bayyana cewa ya samu adadin yawan ‘yan majalisan kasar da yake bukata domin ya lashe zabe na Watan Yuni.

Femi Gbajabiamila ya bayyana wannan ne ta bakin shugaban kwamitin yakin neman zabenna sa watau Honarabul Abdulmumin Jibrin, a lokacin da yake magana da wasu manema labarai jiya Ranar Talata 15 ga Watan Mayun 2019.

KU KARANTA: Tinubu: Babu gudu babu ja-da-baya a kan kalaman da nayi – El-Rufai

Zaben Majalisa: ‘Dan Majalisar APC Gbajabiamila ya samu goyon baya mai rinjaye

Jibrin yace Gbajabiamila ya ba Abokan hammayarsa tazara
Source: Twitter

Abdulmumin Jibrin ya kara da cewa yanzu ta kai Gbajabiamila yana kokarin zama ne da kakakin majalisa Yakubu Dogara, da kuma tsofaffin kakakin majalisa na kasar da aka yi, da kuma manyan ‘yan adawa da ke majalisar kasar.

Haka zalika Jibrin ya bayyanawa ‘yan jarida cewa shugaban masu rinjaye a majalisar, Femi Gbajabiamila mai neman kujerar Rt. Hon. Yakubu Dogara, zai samu ya hadu da sauran Abokan hamayya da ke harin wannan kujera.

Yanzu haka dai Femi Gbajabiamila ya kammala lissafinsa inda ya zabi Hon. Ahmed Wase ya tsaya tare da shi a matsayin mataimakin shugaban majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel