Wiwi: Najeriya za tayi asarar biliyoyi a kasuwannin Duniya - Akeredolu

Wiwi: Najeriya za tayi asarar biliyoyi a kasuwannin Duniya - Akeredolu

Mun samu labari cewa mai girma gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu SAN, yayi kira ga Najeriya ta shiga cikin kasuwar tabar wiwi, ko kuma ta rasa makudan kudin da ake samu a Duniya.

Gwamna Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa Najeriya tana gaf da asarar kudi har Dala Biliyan 145 a Duniya idan tayi watsi da harkar noma halataciyyar tabar wiwi. Gwamnan na APC ya bayyana wannan ne a shafin sa na Tuwita.

Rotimi Akeredolu ya nuna cewa muddin Najeriya ta guji noman wiwi da ake yi a kasashen Duniya, za ta rasa wadannan makudan kudi da ya kamata ace ta samu daga yanzu zuwa shekarar 2025, don haka ya gargadi kasar ta sake nazari.

KU KARANTA: Abin da Gwamnan Jihar Anambra ya tattauna da Buhari

Wiwi: Najeriya za tayi asarar biliyoyi a kasuwannin Duniya - Akeredolu
Gwamna yana so a shiga harkar noma ganyen wiwi a Najeriya
Asali: UGC

Kamar yadda mu ka samu labari, gwamnan yayi wannan magana ne bayan ya tafi kasar Thailand, inda ya ga yadda ake noman ganyen wiwi iri-iri a kasar. Akeredolu yana ganin cewa wiwi zai yi kyau idan aka shuka sa a jihar sa.

Gwamnan na Ondo yace gwamnatin sa za tayi kokarin wajen dagewa da noma ganyen wiwi, wanda za a rika amfani da shi wajen hada magani. Gwamnan yake cewa hukumar NDLEA mai kula da kwayoyi za ta rika kula da wannan aiki.

Gwamna Akeredolu yake cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta ba harkar noman wiwin muhimmanci domin bunkasa tattalin arziki da kuma samawa Matasan kasar aikin-yi. Gwamnan ya ziyarci Thailand ne tare da shugaban NDLEA.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel