Abinda ake gudu ya afku: Zirga-zirga ta ragu a fadar sarkin Kano

Abinda ake gudu ya afku: Zirga-zirga ta ragu a fadar sarkin Kano

- Rahotanni sun nuna cewa zirga zirga ta ragu sosai a fadar sarkin Kano tun bayan da aka kammala kadamar da sababbin masarautun guda hudu a fadin jihar

- Sannan mun samu rahoton cewa tun bayan dawowar sarkin daga kasa mai tsarki ya kadaice kanshi a daki baya magana da kowa

Zirga-zirga ta ragu a fadar Sarkin Kani, Muhammad Sanusi II, bayan kaddamar da sababbin masarautun yanka guda hudu da gwamna Ganduje ya yi wanda suka hada da Bichi, Rano, Karaye da kuma Gaya.

Ranar Lahadin da ta gabata fadar a cike take da al'umma a lokacin da sarkin ya dawo daga aikin Umrah, inda dubunnan mutane suka fito suna yi mishi barka da zuwa a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Mutanen sun biyo shi har zuwa fadar shi daga filin jirgin, inda suke yi mishi kirarin 'Sarki Mai Martaba'.

Abinda ake gudu ya afku: Zirga-zirga ta ragu a fadar sarkin Kano
Abinda ake gudu ya afku: Zirga-zirga ta ragu a fadar sarkin Kano
Asali: Facebook

Mun samu labarin cewa a yau Talatar nan zirga-zirga ta ragu sosai a fadar, duk yawan zirga-zirgar da aka saba gani a fadar ta mutane da ababen hawa komai ya ragu.

Mutane kalilan ne suka rage a fadar sai ma'aikatan fadar.

Wani Dogari wanda ya yi magana da manema labarai ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da cewar sarkin ya zabi ya kadaice kanshi tun dawowar shi daga kasa mai tsarki.

KU KARANTA: Matsalar tsaro: 'Yan bindiga sun kai hari jihar Kebbi

Ya ce: "Tun dawowar Mai Martaba, bai sake magana ba. Ya samu ganin baki kalilan ne da suke zuwa ziyartar shi. Manema labarai da yawa sun zo domin yin hira da shi amma ya hana kowa ganinshi.

"Wannan kirkiro sabbin masarautu ya shafi yawaitar zirga-zirga a fadar nan, kuma ina mai tabbatar muku cewa Mai Martaba bai ji dadin abinda ya faru ba."

A cewar shi, Dogarai da yawa da suke fadar Sarkin Kanon sun bar fadar zuwa sauran masarautun da aka kirkira, musamman ma masarautar Bichi inda dan gidan Marigayi Ado Bayero ke Mulka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel