Matsalar tsaro: 'Yan bindiga sun kai hari jihar Kebbi

Matsalar tsaro: 'Yan bindiga sun kai hari jihar Kebbi

- Wasu 'yan ta'adda sun kai hari wani kauye a jihar Kebbi

- 'Yan ta'addar da ke dauke da manyan makamai sun kai harin, inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi

- Sai dai rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addar basu kashe ko mutum daya ba, amma su sanya mutanen garin yin hijira domin tsira da rayukansu

Wasu 'yan ta'adda akan babur guda biyar sun kai hari garin Illo da ke karamar hukumar Bagudu cikin jihar Kebbi jiya Litinin da dare.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya samu rahoton cewa 'yan ta'addar sun kai harin dauke da manyan makamai, inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi, hakan ya tilasta al'ummar kauyen neman mafaka domin tsira da rayuwarsu.

Haka kuma rahotanni sun nuna cewa ba ayi asarar rai ba, amma 'yan ta'addar sun tilasta mutane da yawa barin kauyen domin tsira da rayukansu.

Matsalar tsaro: 'Yan bindiga sun kai hari jihar Kebbi
Matsalar tsaro: 'Yan bindiga sun kai hari jihar Kebbi
Asali: Twitter

A lokacin da aka tuntube shi, shugaban karamar hukumar Bagudo, Alhaji Muhammad Kaura, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 11:30 na daren Litinin.

"Mun ga 'yan ta'addar da yamma suna ta yawo a cikin gari suna sayen burodi, lemo da ruwa, amma babu wanda ya nuna ya damu dasu ballantana ya kai ga kai su kara," in ji shi.

Kaura ya ce daga baya 'yan ta'addar suka kai hari ga al'ummar kauyen, ya kara da cewa lokacin da 'yan kungiyar sa kai da mutanen kauyen suka taso musu, sai suka fito da manyan makamai suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

KU KARANTA: Wani matashi ya aika da kaninshi lahira

"A lokacin ne al'ummar kauyen suka fara neman mafaka domin tsira da rayukansu.

"Babu wanda aka sace, ko aka harba a harin da suka kawo."

Shugaban karamar hukumar ya bukaci mutane garin da su sanya ido, su kuma kai rahoton duk wani mutumi da ba su yadda dashi ba a garin.

"Komai ya daidai ta yanzu, mutanen gari kowa ya koma harkokinsa," in ji shugaban karamar hukumar.

A lokacin da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, ya ce, "ku yi hakuri zan dawo gareku."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng