Shugaban NDLEA da Gwamnan Ondo sun tafi kasar Thailand don gano yadda ake shuka tabar wiwi

Shugaban NDLEA da Gwamnan Ondo sun tafi kasar Thailand don gano yadda ake shuka tabar wiwi

Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu tare da shugaban hukumar yaki da fatauci da ta’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA, Muhammad Mustapha Abdallah sun tafi kasar Thailand don gano yadda ake noma ganyen tabar wiwi.

Legit.ng ta ruwaito Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata, 14 ga watan Mayu a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda yace suna neman wannan ilimi ne don bunkasa hanyoyin samar ma jahar kudaden shiga ta hanyar noma tabar wiwi tare da amfani dashi ta hanyar daya kamata.

KU KARANTA: Kotu ta hana Magu ya gudanar da bincike akan Adams Oshiomole

Shugaban NDLEA da wani Gwamna sun tafi kasar Thailand don gano yadda ake shuka tabar wiwi

Shugaban NDLEA da Gwamnan
Source: UGC

Gwamnan ya kara da cewa tawagarsu zata karanci dabarun noma tabar wiwi don yin magunguna tare da samun kudin shiga ne sakamakon jahar Ondo ce ta daya wajen noma tabar wiwi a Najeriya, kuma ana sa ran samun dala biliyan 145 a kasuwar hada hadar wiwi zuwa shekarar 2025.

“Don haka ba karamar asara zamu tafka ba idan bamu shiga wannan harkar an dama damu ba.” Inji Gwamna Rotimi Akeredolu a yayin jawabin daya gabatar lokacin da suke rangadin wani kamfanin dake sarrafa tabar wiwi.

Shugaban NDLEA da Gwamnan Ondo sun tafi kasar Thailand don gano yadda ake shuka tabar wiwi

Akeredolu
Source: Twitter

Gwamnan bai tsaya nan sai da yace: “Zamu karkatar da hankulanmu zuwa ga amfani da tabar wiwi ga kiwon lafiya tare da hada magunguna, duka wannan zamu yi shine a karkashin sa’idon hukumar NDLEA, don haka nake kira ga gwamnatin tarayya ta duba yiwuwar zuba jari a harkar don samar ma matasa ayyukan yi.”

Idan za’a tuna mun kawo muku rahoton dake nuna jami’an NDLEA sun kama mutane dubu tara da dari takwas da ashirin da hudu, 9,824 a cikin shekarar 2018 kadai akan tuhume tuhumen laifukan da suka shadi ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel