Kotu ta hana Magu ya gudanar da bincike akan Adams Oshiomole

Kotu ta hana Magu ya gudanar da bincike akan Adams Oshiomole

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta haramta ma hukumar dake yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, gudanar da binciken zargin almundahana akan shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia Anwill Chikere ce ta yanke wannan hukunci a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, inda tayi fatali da bukatar da EFCC ta shigar gabanta na samun daman binciken Adams Oshiomole.

KU KARANTA: Satar mutane: Hanyar Kaduna-Abuja tayi lafiya – El-Rufai ga matafiya

Kotu ta hana Magu ya gudanar da bincike akan Adams Oshiomole
Kotu ta hana Magu ya gudanar da bincike akan Adams Oshiomole
Asali: UGC

Lauyan EFCC, Uju Chukwura ya bayyana ma kotun cewa sashi na 6 na kundin dokokin hukumar ya bata damar gudanar da binciken duk wani dan Najeriya da ake zargi da satar kudin jama’a, kuma kotun ta yarda da hakan.

Sai dai Alkalin kotun ta bayyana cewa EFCC bata da hurumin gudanar da bincike akan Oshiomole duba da cewa ta wuce kwanaki 90, ma’ana watanni 3 da dokar ta tanada don shigar da irin wannan kara, bata shigar da karar ba sai bayan watanni 18, da wannan ne kotun ta dakatar da EFCC daga binciken Oshiomole.

Hukumar EFCC dai tana tuhumar Oshiomole ne da wadaka tare da bindiga da kudaden jama’a yayin da yake rike da mukamin gwamnan jahar Edo, haka zalika hukumar na zarginsa da sayan kadarori a kasashen Amurka, Afirka ta kudu da Dubai, sai kuma wani gida daya gina na naira biliyan 10 a kauyensu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng