Gasar Yammacin Afrika: Nijar ta sha kashi 15-0 a hannun Najeriya

Gasar Yammacin Afrika: Nijar ta sha kashi 15-0 a hannun Najeriya

Kungiyar kwallon kafa na Matan Najeriya watau Super Falcons sun ragargaji Takwaransu Makwabta na kasar Nijar da ci 15 a wani wasa da aka buga a Gasar cin kofin Yankin Nahiyar Yammacin Afrika.

Kamar yadda mu ka samu labari, ‘Yan wasan Super Falcons din su doke Nijar ne da ci 15-0 a Gasar da ake bugawa a cikin babban birnin Abidjan da ke kasar Cote d’Ivoire. An fara dirkawa kasar Nijar ci ne tun a minti 9 da take wasan.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci ne aka zubawa Kasar Nijar kwallaye 9 a cikin raga. Wannan nasarar da ‘Yan kwallon Najeriya su ka samu, yana nufin Matan sun samu karasawa zuwa zagaye na gaf da wasan karshe a wannan gasa.

KU KARANTA: ‘Yan kwallon Afrika sun lashe kyautar takalmin gwal a Ingila

Gasar Yammacin Afrika: Nijar ta sha kashi 15-0 a hannun Najeriya
Najeriya ta lallasa Nijar da ci 15 da nema a Gasar kofin Mata
Asali: Twitter

Yanzu haka dai Super Falcons ce ke rike da kambun Yammacin Afrika. ‘Yan wasan na Najeriya za su kuma kara da kasar Mali domin samu zuwa wasan karshe na gasar. Najeriya za ta so ta sake lashe gasar wannan shekarar da ake yi.

‘Yan matan na Najeriya sun yi wa Nijar wannan ragargaza ne a Ranar Asabar din da ta gabata watau 11 ga Watan Mayu. Kafin nan Super Falcons din sun doke kasar Burkina Faso da ci 5-1 a Ranar Alhamis kafin arangama da kasar Nijar.

Wannan yana cikin shirin da Matan na Najeriya su ke yi na shiga gasar cin kofin Mata na Duniya wanda za a fafata a kasar Faransa. Za a doka wannan Gasa ne a cikin Watan Yuni zuwa Yulin shekarar bana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel