Kotu ta kori karar dan takarar jam'iyyar PDP a Kano

Kotu ta kori karar dan takarar jam'iyyar PDP a Kano

Kotun daukaka kara, dake zamanta a kan titin Miller dake unguwar Bompai a birnin Kano, ta kori karar da dan takarar majalissar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa na jamiyar PDP a zaben 2019 daya gabata, Hon. Munnir Dahiru, ya shigar gabanta.

PDP da dan takarar ta sun shigar da karar ne domin kalubalantar nasarar da jamiyar APC tare da wanda yayi mata takara, Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe, suka samu.

Kotun ta kori karar ne bisa rashin cikakkun hujjojin da Jamiyar PDP tare da dan takarar ta suka gaza gabatarwa yayin zaman kotun na ranar Litinin.

Jamiyar PDP tare da dan takarar ta Barista Munir Dahiru sun shigar da karar ne bisa rashin Nasarar da Suka Samu a zaben gaya Gudana, wanda jam'iyyar APC tare da dan takarar ta Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe suka samu nasarar lashe wa da gagarumin rinjaye.

Kotu ta kori karar dan takarar jam'iyyar PDP a Kano

Munir Dahiru; dan takarar jam'iyyar PDP a Kano
Source: Facebook

Yayin da Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe ya samu kuri'a dama da dubu sittin da shida (66,000) shi kuma Munnir Dahiru na Jamiyar PDP ya samu kuria dubu talatin da biyu (32,000) da doriya.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi ganawar sirri da wasu gwamnoni uku

A wata kididdiga da Rabiu Muhd Ibrahim, dan jam'iyyar APC, ya yi, ta nuna cewa Tijjani Abdulkadir Jobe na Jamiyar APC ya ninninka Munir Dahiru na Jamiyar PDP da yawan kuri'u masu daraja ta daya.

"Kazalika, masana bincike a kan harkokin zaben da ya gabata suka tabbatar tare da yin ittifakin cewar kaf Jihar Kano da Najeriya, babu dan majalissar tarayya a zaben 2019 wanda ya samu yawan kuri'un da Tijjani Abdulkadir Jobe ya samu," a cewar Rabi'u, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel