Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon (Bidiyo)

Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon (Bidiyo)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) a fadar shugaban kasa dae Abuja.

Gowon ne mutum na biyar daga cikin manyan kasar nan da suka ziyarci Buhari a fadar gwamnatin tarayya a ranar Litinin.

Gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, ne ya fara ziyartar shugaba Buhari domin yi masa godiya a kan sake zabensa da ya yi domin cigaba da zama babban gwamnan CBN.

Bayan ziyarar Emefiele, gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya ziyarci shugaba Buhari, inda suka yi wata ganawar sirri.

Daga bisani gwamnonin jihohin Kaduna; Malam Nasir El-Rufa'i, da Benuwe; Samuel Ortom, sun ziyarci shugaba Buhari tare da yin ganawar sirri. Gwamnonin sun ziyarci Buhari a lokuta daban-daban.

DUBA WANNAN: Abinda yasa Ganduje bai tsige sarki Sanusi II ba - Majiyar gwamnatin Kano

Dukkan gwamnoni sun gana ne da Buhari a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu.

Babu wani jawabi da fito dangane da dalilin ziyarar da gwamnonin da Gowon suka kai wa Buhari ba, kazalika ba samu labari a kan abinda suka tattauna ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel