Tarin motocin alfarma: Me zaka fada ma Allah – Gudaji Kazaure ya tambayi Dino Melaye

Tarin motocin alfarma: Me zaka fada ma Allah – Gudaji Kazaure ya tambayi Dino Melaye

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni da yan kwashi, Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana kidimewarsa yayin da yaga tarin motocin alfarma da Sanata Dino Melaye ya tara a gidansa, kuma dukkaninsu na hawa ne.

Legit.ng ta ruwaito a makon data gabata ne Gudaji ya kai ma Dino Melaye ziyarar ta’ziyya bisa mutuwar mahaifiyarsa, indsa yaje gidansa domin ya jajanta masa, daga bisani kuma ya leka garejin motocin Dino don game ma idanunsa.

KU KARANTA: Buhari ya yi ma wata kyakkyawar budurwa mai shekaru 27 nadin mukami mai muhimmanci

Shi dai Dino mutum ne da yayi kaurin suna wajen hawa manya manyan motocin alfarma, inda ya bayyana cewa shi mutum ne mai sha’awar motocin alfarma, kamar dai yadda Hausawa ke cewa shan koko daukan rai.

Sai dai cikin wasa da raha, Gudaji ya gargadi Dino kan me zai fada ma Allah a gobe kiyama game da mallakar wadannan motoci, yayin da dubun dubatan jama’an da yake wakilta suke cikin matsanancin talauci?

Gudaji yace idan da shine sayar da motocin zai yi duka ya saya ma jama’ansa abinci, domin kuwa a cewarsa talakawa ne a gabansa, kuma idan da yana da naira miliyan dari, toh zai kashe ma talakawa miliya tamanin.

A lokacin da ya kirga tafka tafkan motocin alfarma guda goma sha daya sai yace “Wallahi Allah zai tambayeka, ba zan iya barci ba idan ni na mallaki motocin nan, zama zan yi inyi ta tunani, watakilama na zare gaba daya saboda ban san me zan fada ma Allah ba.” Inji shi

Daga karshe ya shawarci Dino Melaye daya more a duniya, idan ya mutu shikenan, Dino ya amsa da cewa da mai rai ake yi dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel