Matakai 5 da muka dauka domin magance matsalar tsaro a Najeriya - Fadar shugaban kasa

Matakai 5 da muka dauka domin magance matsalar tsaro a Najeriya - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta lissafa matakai daban-daban da ta dauka daga watan Janairu zuwa yanzu domin kawo karshen aiyukan ta'addanci da suka jefa kasa cikin matsalar tsaro, tare da bayar da tabbacin cewar za ta ga bayan dukkan masu nufin Najeriya da sharri.

Da yake lissafa matakan da gwamnatin Buhari ta dauka a ranar Lahadi a Abuja, kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewar gwamnatin tarayya ta dukufa wajen kawo karshen kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta.

"Gwamnatin Buhari a shirye take domin daukan matakan da zasu kawo karshen matsalolin tsaro a kasar nan, za mu yi galaba a kan dukkan masu nufin Najeriya da sharri," a cewar Adesina.

Sannan ya jero matakan da gwamnati ta dauka domin magance kalubalen tsaro a sassan kasar nan, wadanda suka hada da; atisayen 'Puff Adder' na rundunar 'yan sanda, atisayen 'HARBIN KUNAMA III na rundunar soji, atisayen 'Egwu Eke 3' na rundunar soji wadanda aka kirkira a cikin shekarar 2019 domin kara karfin atisayen 'sharan daji' na rundunar soji da aka kirkira a shekarar 2016 da atisayen 'diran mikiya' na rundunar soji da aka kirkira a shekarar 2018.

Matakai 5 da muka dauka domin magance matsalar tsaro a Najeriya - Fadar shugaban kasa
Buhari na gaisawa da Adesina bayan dawowar sa daga kasar Ingila
Asali: Twitter

Adesina ya kara da cewa; "dukkan wadannan matakai an kirkire su ne domin magance aiyukan 'yan bindiga da 'yan ta'adda a arewa maso yamma."

DUBA WANNAN: Sabbin Sarakuna: Mun yiwa dokar garambawul, babu mai iya canja ta - Ganduje

A cewar sa, alhakin gwamnati ne ta tabbatar da tsaron lafiyar jama'ar ta da dukiyoyinsu kamar yadda kundin tsarin mulkin ya tanada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel