Dakaru sun halaka 'yan Boko Haram 4 a Maiduguri

Dakaru sun halaka 'yan Boko Haram 4 a Maiduguri

Yayin wani farmaki na kwanton bauna da dakarun sojin kasan Najeriya su ka kai cikin wasu kauyuka a jihar Borno, tsugune ta karewa wasu 'yan kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram 4 da tuni suka riga mu gidan gaskiya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, kakakin bataliyar sojin kasa, Kanal Sagir Musa, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Lahadi, 12 ga watan Mayun 2019 cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Dakaru sun halaka 'yan Boko Haram 4 a Maiduguri

Dakaru sun halaka 'yan Boko Haram 4 a Maiduguri
Source: Facebook

Kanal Musa ya bayyana cewa, dakarun sojin kasan tare da hadin gwiwar dakarun tsaro na sa kai, sun kai farmaki na tankade da rairaya a yankunan da 'yan ta'adda ke cin karen su babu babbaka da suka hadar da kauyukan Surdewalla, Ranwa, Baladayo, Sabon Gari da kuma Shetimeri.

A yayin da kimanin sojoji biyu suka jikkata yayin dauki ba dadi da masu tayar da kayar baya, Kanal Musa yayi karin haske dangane da yadda wata Bataliyar sojin kasa mai lamba 177 tare da hadin kungiyar dakarun tsaro na sa kai suka tashi sansanan 'yan ta'adda a kauyukan Mboa, Mboa-Kura, Yarchisa, Bombula, Tshata da kuma Bamzir.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, Bataliyar sojin kasa mai lamba 121 da kuma 192 tare da hadin gwiwar dakarun tsaro na 'yan sa ka ta samu nasarar hallaka 'yan boko haram da dama yayin wani farmaki na kwanton bauna da ta kai cikin kauyukan jihar Borno a ranar Juma'a.

KARANTA KUMA: Babu abinda Buhari ya fi ba muhimmanci irin inganta jin dadin al'umma - Osinbajo

Kamar yadda kididdigar rahotanni ta bayyana, ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram da ta shafe tsawon shekaru goma ta na tafka ta'asa a kasar nan ta salwantar da rayukan kimanin Mutan dubu ashirin da takwas yayin da sama da miliyan biyu suka rasa muhallan su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel