Huduba: Abubuwan da za a dage da su a lokacin Azumin Watan Ramadan

Huduba: Abubuwan da za a dage da su a lokacin Azumin Watan Ramadan

Yayin da ake cikin Wata mai alfarma na Azumi a fadin Duniya, Malaman addinin Musulunci su na cigaba da fadakar da kan al’umma a game abubuwan da su ka shafi Azumin Watan Ramadan.

A jiya Juma’a 6 ga Watan Ramadan, Limamin Masallacin ITN da ke cikin Zariya a Jihar Kaduna, Dr. Mustapha Isa Qasim yayi huduba a kan wasu ibadu da ya kamata a runguma a wannan Wata.

Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin wadannan ibada na musamman:

1. Sallah a Jami’i

Akwai falala mai yawa a rika tsaida sallah yadda ya kamata a cikin wannan Wata, kuma musamman sallah a jami’i. Ana so ya zama Musulmi yana riskar kabbarar farko ta kowace sallah.

2. Karatun Al-Qur’ani

Haka zalika, jaratun Al-Qur’ani abu ne mai matukar lada musamman a wannan Wata. Zai yi kyau mutum ya sauke Al-Qur’ani ko sau daya har zuwa sau 7 ko kuma gwargwadon iyawar sa a Ramadan.

3. Taimakon juna

Wani abu mai fa’ida a wannan Wata shi ne taimakawa ‘yan uwa Musulmi marasa karfi a Watan Azumi. Za a so masu karfi su rika daukar nauyin ciyar da Bayin Allah wadanda ba su da wadata.

4. Tsayuwar dare (Tarawih da Tahajjud)

Abu ne mai kyau mutum ya dage wajen tsayuwar Sallar dare a Ramadan. Sallolin Qiyam Layl na Tarawihi da Tahajjud da ake yi a cbangarorin dare su na sa a a yafewa mutum zunuban da yake da su.

KU KARANTA: Abubuwa 5 da aka haramtawa duk wani Mai Azumi

5. Laylatul-Qadr

Bayan haka, abu ne mai matukar riba a dagewa ibada dare-da-rana a cikin kwanaki goma-na-karshe. A wannan kwanaki ne Malamai su ka hadu a kan cewa ana dacewa da daren Laylatul-Qadr.

6. I’titikafi

Daga cikin ibada masu matukar lada kuma a Watan nan na Ramadan akwai I’itiqafi, wanda mutum zai tare a Masallaci ya karkata wajen bautar Allah babu kaukautawa na tsawon wani lokaci.

7. Addu’o’i

An kuma so mai azumi a bakinsa ya dage da yin addu’o’i da za su sanya a yafe masa zunubansa ko kuma har ya shiga cikin jerin Bayin da Ubangiji zai ‘yanta a cikin Wannan Wata mai alfarma.

8. Rangwame

Wani abu mai muhimmanci a lokacin Azumi shi ne ya zama Musulmai sun samawa jama’a saukin rayuwa wajen rage farashin kaya da kudin aiki domin al’umma su samu sauki da neman samun babban rabo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng