Tirkashi: Fateema Ganduje ta caccaki masu zagin mahaifinta akan sabbin masarautu

Tirkashi: Fateema Ganduje ta caccaki masu zagin mahaifinta akan sabbin masarautu

- Ba wannan ne karo na farko da 'yar gidan gwamnan jihar Kano, Fateema Abdullahi Umar Ganduje, ta fara caccakar mutane akan mahaifinta ba

- Ta bayyana abinda mahaifin nata ya yi a matsayin adalci ga garuruwan da ba a yi musu adalci ba a baya

Tun bayan lokacin da mahaifinata, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kuduri niyyar kirkirar sababbin masarautu guda hudu, ta dinga yin rubutu da tura bidiyo kala-kala a shafukanta na sada zumunta.

"Tun da can akwai Sarakunan Rano, Gaya da Karaye sama da shekaru 1000 da suka shude. Rano na daya daga cikin garuruwan da Shehu Usman Danfodio ya turo mayakanshi domin su kwato ta, shekaru hudu bayan bayan fulani sun kwace Kano a shekarar 1807. Hakazalika Rano na daya daga cikin garuruwan 'Hausa Bakwai'. Hakan da aka yi ba komai bane illa adalci ga garuruwan da aka tauye musu hakkinsu a baya."

Tirkashi: Fateema Ganduje ta caccaki masu zagin mahaifinta akan sabbin masarautu

Tirkashi: Fateema Ganduje ta caccaki masu zagin mahaifinta akan sabbin masarautu
Source: Twitter

Fateema ta tura wannan labarin a shafinta na Instagram inda take nuna cewa Ganduje ya kirkiro sabbin masarautun hudu ne don "tabbatar da adalci ga garuruwan da aka tauye hakkinsu a baya."

Sai dai kuma ta dinga samun zokaci daga abokanan ta na shafukan sada zumunta. A cikin daya daga cikin rubutun da ta dora a shafinta, ta ba da misali game da rubutun da 'yar gidan Sarkin Kano ta yi, inda take bayyana Ganduje a matsayin babban bala'in da Allah ya turo jihar Kano.

KU KARANTA: 'Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi

"Kun ga rubutu na amma ba ku ga rubutun da 'yar shi ta yi ba. Kuna nan baku da aiki sai suka na, ni kuma ina nan ina shan dariya," in ji Fateema.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel