Yadda wani ya aikata ma Fulani danyen aiki yayi awon gaba da garken shanunsu duka

Yadda wani ya aikata ma Fulani danyen aiki yayi awon gaba da garken shanunsu duka

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Ilori ta bada umarnin garkame wani dan Fulani makiyayi mai suna Muhammadu Usman sakamakon kararsa da aka shigar gabanta inda ake zarginsa da kashe wasu makiyaya biyu yan gida daya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin Kotun, mai sharia Oluwabukola Oreoluwa yayi fatali da bukatar da Usman ya mika masa na neman beli, don haka ya bada umarnin a daure masashi a gidan yarin Oke-Kura dake garin Ilori har sai ya ji daga bakin babban jami’I mai shigar da kara na jahar Kwara.

KU KARANTA: Shariff Rabiu Usman Baba: Muhimman batutuwa 10 game da rayuwarsa

Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Isaac Yakubu ya shaida ma kotun cewa wanda ake zargi Muhammadu Usman ya kashe makiyaya biyu yan Fulani kuma yan gida daya, Usman Abdullahi da Salihu Abdullahi a kauyen Elemere dake cikin karamar hukumar Moro, sa’annan yayi awon gaba da shanunsu.

Dansandan ya kara da cewa a daidai hanyar zuwa Malete aka kama Muhammadu Usman yayin da yake kokarin arcewa da garken shanun. Da wannan ne rundunar Yansanda take tuhumarsa da laifin kisan kai da kuma fashi da makami, laifukan da suka saba ma sashi na 221 na kundin hukunta manyan laifuka.

Daga karshe kuma ya nemi Alkali kotun da kada ya baiwa Muhammadu Usman beli saboda girman laifukan da ake tuhumarsa dasu, ya kara da cewa basu kammala gudanar da bincike akansa ba.

Jin haka, tare da jiran sauraron umarnin babban jami’I mai shigar da kara na jahar Kwara ne, yasa Alkali Oreoluwa dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Mayu.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Legas ta sanar da gano gawarwakin wasu Hausawa guda hudu masu sana’ar canjin dala da aka kashe, a cikin wani matattara tara kashi dake unguwar Ikorodu ta jahar Legas.

Rundunar Yansandan ta bayyana cewa wasu yan damfara ne suka kashe mutanen hudu bayan sun damfaresu makudan kudade a ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2019, inji kaakakin Yansandan jahar, DSP Bala Elkana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng