Ashe jami'an 'yan sandan dake jihar Lagos kasuwanci suke zuwa yi ba aiki ba

Ashe jami'an 'yan sandan dake jihar Lagos kasuwanci suke zuwa yi ba aiki ba

- Za a canjawajami'an hukumar 'yan sanda dubu shida wurren aiki daga jihar Lagos zuwa jihohin da ake fama da matsalolin tsaro a kasar nan

- Shugaban hukumar ya ce zai yi hakan ne saboda ya fuskanci cewa da yawa daga cikin jami'an da suke jihar Lagos din ba aikin da aka dauke su suke zuwa yi ba, suna zuwa jihar kasuwanci ne

Shugaban hukumar 'yan sanda na kasa, Mohammed Adamu ya bada umarnin dauko jami'an 'yan sanda sama da dubu shida daga jihar Lagos a dawo dasu jihar Zamfara, da sauran jihohi da ake fama da matsalar tsaro a kasar nan.

Bisa ga rahoton da muka samu, shugaban zai yi hakan ne domin kawo gyara ga jami'an 'yan sandan dake jihar ta Lagos, da kuma kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi wasu jihohi a kasar nan.

Bayan haka kuma an bayyana cewa, mafi yawan jami'an 'yan sandan dake jihar ta Lagos, sun mayar da jihar wurin shakatawa da kuma gabatar da harkokin kasuwancin su, maimakon su yi aikin da ya kai su.

Ashe jami'an 'yan sandan dake jihar Lagos kasuwanci suke zuwa yi ba aiki ba
Ashe jami'an 'yan sandan dake jihar Lagos kasuwanci suke zuwa yi ba aiki ba
Asali: Original

A lokacin da aka fara gabatar da wannan tsarin, an canjawa jami'an hukumar kimanin 1,001 wurin aiki daga jihar Lagos zuwa wasu jihohi a fadin kasar nan.

Jami'an da abin zai shafa sun hada da, Assistant Superitendent of Police, Deputy Superitendent of Police, Superitendent of Police da kuma Chief Superitendent of Police.

Bayan an kammala canjawa wadannan wurin aikin, ana tunanin shugaban hukumar zai kara canjawa jami'an hukumar kimanin 5,000 wurin aiki.

A wata takarda da ya fitar ranar 2 ga watan Mayu, 2019, shugaban ya umarci jami'an da ya canjawa wurin aikin da su gaggauta komawa jihohin da aka canja musu.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Akwai yiwuwar tafiya yajin aiki a fadin Najeriya

Jihar Zamfara, wacce ke fama da matsalar tsaro, an tura mata jami'ai 50 daga jihar Lagos.

Sannan an tura jami'ai 22 zuwa jihar Abia.

Sauran jihohin sun hada da Adamawa 43, Akwa Ibom 11, Anambra 9, Bauchi 31, Benue 32, Borno 24, Bayelsa 14, Cross River 20, Delta 10, Ebonyi 43, Ekiti 42, Enugu 29 da kuma babban birnin tarayya Abuja da aka tura mata jami'ai guda 5.

Bayan haka kuma akwai wasu jihohin da suka hada da Gombe 24, Imo 30, Jigawa 34, Kebbi 47, Kaduna 35, Kogi 23, Kano 32, Katsina 41, Kwara 20, Nasarawa 22, Niger 14, Ondo 14, Osun 26, Oyo 41, Plateau 32, Rivers 37, Sokoto 29, Taraba 40, Yobe 35.

An canja jami'an da aka dauke daga Lagos din da wasu jami'an na wasu jihohi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel