Kisa da kona gidaje: Hotunan barnar da mayakan Boko Haram suka tafka a Molai
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe mutane 9 a wasu hare-hare da biyu da suka kai a yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun kone kauye guda tare da sace manona uku, kamar yadda mahukunta da 'yan sintirin 'sa kai' suka sanar ranar Laraba.
Mayakan sun dira a kauyen Molai a cikin motoci tare da kai hari kan jama'a da yammacin ranar Talata, daf da lokacin da jama'a ke shirin shan ruwan azumin watan Ramadana.
Mambobin kungiyar da ake kyautata zaton masu biyayya ga shugabancin Abubakar Shekau ne, sun kashe mutane 6 tare da kona gidaje fiye da 12.
Usman Kyari, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Borno, ya ce sun dauki gawar mutane shida bayan harin da mayakan na Boko Haram suka kai. Dukkan su an harbe su ne.
"Mayakan sun kone gidaje kusan 40 bayan barnar dukiyar jama'a da suka yi," a cewar Kyari.
Mayakan kungiyar Boko Haram suna yawan kai hari garin Molai mai nisan kilomita biyar daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
DUBA WANNAN: Bayan 'sa hannun' Ganduje: Jerin kananan hukumomin dake karkashin masarautun Kano 5
Sai dai daga baya rundunar sojin sama tayi luguden wuta a yankin, lamarin da ya saka mayakan tsere wa.
A wani harin na daban, mayakan Boko Haram sun kashe manoma uku a garin Konduga, mai nisan kilomita 38 daga Maiduguri, a cewar shugaban 'yan kungiyar sintirin 'sa kai', Ibrahim Liman.
"Mayakan sun yiwa manoman yankan rago kafin su jibe gawarwakin su," Liman ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng