Garkuwa da Mutane: Likitoci za su kauracewa aiki a jihar Kuros Riba

Garkuwa da Mutane: Likitoci za su kauracewa aiki a jihar Kuros Riba

Akwai yiwuwar nan ba da jimawa ba Likitoci a jihar Kuros Riba da ke Kudancin kasar nan za su yiwa aiki kaura a sakamakon ci gaba da ta'azzarar aukuwar ta'addancin masu garkuwa da mutane akan abokanan su na aiki.

Garkuwa da Mutane: Likitoci za su kauracewa aiki a jihar Kuros Riba
Garkuwa da Mutane: Likitoci za su kauracewa aiki a jihar Kuros Riba
Asali: UGC

Dakta Agam Ayuk, shugaban kungiyar Likitoci na jihar Kuros Riba tare da sakataren kungiyar, Dakta Ezoke Epoke, cikin wata sanarwa da suka rattabawa hannu bayan taron kungiyar su da ya gudana, sun yanke hukuncin cewa ba za su ci gaba da sadaukar da rayuwar su ba ga 'yan ta'adda.

A sakamakon kai komo da zirga-zirga wajen sauke nauyin da rataya wuyan su, Likitoci na afkawa cikin tarkon masu garkuwa da mutane musamman a jihar Kuros Riba kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Yayin shimfida wa'adi na kwanaki biyu, Likitoci sun yi kira ga dukkanin hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki a jihar Kuros Ribas, da su gaggauta ceto abokin aikin su, Dakta Ogbonna Uchenna daga hannun masu ta'adar garkuwa da mutane da aka dauke tun a ranar 3 ga watan Mayun 2019.

KARANTA KUMA: Buhari ya gana da shugabannin tsaro cikin fadar Villa

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Dakta Uchenna ya afka tarkon masu ta'adar garkuwa da mutane yayin da ya ke kan hanyar dawowa daga karamar hukumar Ogoja zuwa gidan sa da ke yankin karamar hukumar Obudu.

A sanadiyar ci gaba da aukuwar wannan mummunan cin kashi da kuma barazana a gare su, kungiyar Likitoci a jihar Kuros Riba ta daura damarar kauracewa aiki daga ranar Alhamis, 9 ga watan Mayun 2019 muddin ba a ceto abokin aikin su ba daga hannu masu garkuwa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng