Jabun kaya: 'Yan sanda sun kama wani dan Chana a Kano

Jabun kaya: 'Yan sanda sun kama wani dan Chana a Kano

A ranar Laraba ne rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kano ta gurfanar da wani dan kasar China, Kaka Jao, mai shekaru 35, a gaban wata kotun majistare bayan samun sa bandir 270 na jabun wata atamfa.

Ana tuhumar Jao, mazaunin gida mai lamba 1b a titin Unity a cikin birnin Kano, da hadin baki tare da shigar da kayan jabu kasuwa.

Dan sanda mai gabatar da kara, Asp Yusuf Sale, ya shaida wa kotun cewar wani mai suna Sammani Adamu dake da shago mai lamba 8 a kan titin Unity, ne ya shigar da korafi a ofishin 'yan sanda na cikin birni a ranar 5 ga watan Mayu.

A cewar dan sandan, Adamu ya kama Jao da bandir 270 na atamfofin bogi a lokacin da zai wuce ta kan titin Unity da misalin karfe 12:00 na ranar 5 ga awatan Mayu.

Jabun kaya: 'Yan sanda sun kama wani dan Chana a Kano
'Yan sanda
Asali: Depositphotos

Asp Sale ya kara da cewa atamfofin na dauke da alamar kamfanin Adamu da ya yiwa rijista da sunan "Chigam Baby"

Ya sanar da kotun cewar wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa yayin gudanar da bincike, har ya bayyana cewar wani dan kasuwa ne mai suna Alhaji Idris ya bashi tambarin kamfanin da aka yi amfani da shi wajen buga atamfofin na jabu.

DUBA WANNAN: UCL: Liverpool ta ga bayan Barcelona a wasan zagayen kusa da na karshe

Rundunar 'yan sanda ta ce yanzu haka tana neman Alhaji Idris, wanda ya tsere bayan samun labarin an kama Jao.

Saidai, wanda ake tuhumar ya ki amsa laifinsa, lamarin da ya sa babban alkalin kotun, Aminu Fagge, ya bayar da belinsa a kan kudi N50m da kuma wanda zai tsaya masa.

Mai shari'a Fagge ya umar Jao da wanda zai tsaya masa su ajiye fasfo dinsu na yin bulaguro zuwa kasashen ketare a kotun, sannan daga bisani ya daga sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng