Da duminsa: Ali Janga ya kama aiki a matsayin kwamishinan 'yan sanda a Kaduna

Da duminsa: Ali Janga ya kama aiki a matsayin kwamishinan 'yan sanda a Kaduna

Mr Ali Janga ya kama aiki a matsayin sabon kwamishinan 'yan sanda na jihar Kaduna kamar yadda Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ya sanar a ranar Talata a garin Kaduna.

Sabo ya ce an yiwa Jango canjin wurin aiki zuwa Kaduna ne a ranar 2 ga watan Mayu inda sai maye gurbin CP Ahmad Abdur-Rahman.

A cewarsa, sabon kwamishinan 'yan sandan dan asalin garin Gwoza ne daga karamar hukumar Borno kuma ya yi karatun digiri a fannin lauya a Jami'ar Maiduguri.

Da duminsa: Ali Janga ya kama aiki a matsayin kwamishinan 'yan sanda a Kaduna
Da duminsa: Ali Janga ya kama aiki a matsayin kwamishinan 'yan sanda a Kaduna
Asali: Twitter

Ya shiga aikin dan sanda a masayin Cadet Superintendent a ranar 3 ga watan Mayun 1990.

DUBA WANNAN: MTN ta bawa Sarki Sanusi II babban mukami

An tura shi jihar Oyo bayan ya samu makamin mataimakin superintendent na 'yan sanda kuma daga wannan lokacin ya rike mukammai masu yawa a Najeriya da kasashen ketare.

Kafin yanzu, ya yi aiki a Akwa Ibom, Abuja, Edo, Ogun da Kwara. Ya kuma yi aiki da EFCC da FCIID.

Ya kuma rike mukamin kwamishinan 'yan sanda a jihohin Kogi da Bauchi inda ya jagoranci atisayen Operation Absolute Sanity a hanyar Kaduna zuwa Abuja a 2017.

Sabo ya ce sabon kwamishinan ya kallubalanci dakarun rundunar su sake mayar da hankulan su a kan aikinsu kuma su guji karbar rashawa da sauran abubuwa da ka iya zubar musu da mutunci.

Ya kuma bukaci jami'an 'yan sandan su kasance masu tsoron Allah wurin gudanar da ayyukan su.

Janga ya yi kira ga al'ummar jihar Kaduna rika taimakawa rundunar 'yan sanda da bayyanai masu muhimmanci da zai taimaka musu gudanar da ayyukansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel