Ta tabbata, Farfesa Tijjani Bande ya zama sabon shugaban majalisar wakilan UN
Farfesa Tijjani Mohammed Bande, tsohon shugaban jami'ar Usman Danfodiyo dake Sokoto, ya zama sabon shugaban majalisar wakilan dinkin duniya (UN).
Tun kafin tabbatar da nadinsa, shugabar majalisar mai barin gado, Maria Fermanda Espinosa Garces, ta bayyana cewar Bande na kan hanya dodar domin zama sabon shugaban majalisar wakilan UN.
Ta bayyana hakan ne yayin wata gana wa da da tayi da shugaba Buhari da ministansa na harkokin kasashen ketare a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Kafin samun sabon mukamin, Bande ne wakilin Najeriya na dun-dun-dun a majalisar dinkin duniya.
Bande, tsohon darektan makarantar horon manyan ma'aikata dake Kuru a jihar Filato, haifaffen garin Zagga ne a jihar Kebbi.
DUBA WANNAN: Fatima Bala, makahuwa 'yar baiwa, ta samu tallafi daga gidauniyar kasar Qatar
Yana da shaidar karatun M. A a kimiyyar siyasa daga jami'ar garin Boston a jihar Massachusetts ta kasar Amurka a shekarar 1981, kazalika, ya yi karatun digiri na uku (PhD) a jami'ar Toronto dake kasar Canada a shekarar 1987.
Ya shugabanci jami'ar Usman Danfodiyo dake Sokoto daga shekarar 2004 zuwa 2009.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng