Kura-kurai 10 da musulmai ke aikatawa lokacin azumi
Watan Ramadana watane mai alfarma ga dukkanin musulman duniya, wanda ya ke sanya daukacin musulman duniya gabatar da ibada ta musamman akan wacce suka saba gabatarwa yau da kullum, hakan na faruwa ne saboda irin falalar da ke cikin watan mai alfarma
Sai dai kuma akwai wasu kura-kurai da mutane ke aikatawa saboda rashin isashen ilimin abinda azumin ya ke nufi. Da yawa daga cikin mutane suna aikata wannan laifukan a kullum cikin wannan watan mai alfarma.
Ya kamata mu guji aikata irin wadannan kura-kuran idan har muna so ibadar da muka yi ta samu karbuwa.
Ga jerin kura-kuran mun kawo muku a kasa:
1. Rashin yin salloli biyar a rana
Wasu musulman suna daukar azumi amma ba sa yin salloli biyar da aka farlantawa dukkanin musulmi su yi. Idan har ka yi azumi saboda kaga kowa yana yi amma ka ki yin sallah, to maganar gaskiya ita ce ka sha kishin ruwa da yunwar banza ne. Sallah ta na da matukar muhimmanci a addinin musulunci, barin ta yana iya fitar da mutum daga musulunci.
2. Kin tashi Sahur
Akwai mutanen da ba su son tashi su yi sahur saboda wasu dalilai na su. Wasu sukan ce ba sa iya cin abinci a irin wannan lokacin.
Yin sahur ya na da matukar muhimmanci in ji manzon Allah S.A.W.
3. Cin abinci da ya wuce misali
Wasu mutanen su na cin kowanne irin abinci da ya zo ta gabansu a lokacin yin sahur, su na yin hakan ne a tunaninsu cewa baza su ji yunwa ba idan gari ya waye. Sannan kuma a lokacin buda baki nan ma su na cin abincin da ya wuce kima. Hakan bai halatta ba a addinin.
4. Cinye wuni guda ana dafa abinci
Mata da yawa suna ganin cewa a lokacin azumin watan ramadana, sai sun dafa abinci kala-kala ga iyalansu. Hakan yana sanyawa sun ciye dukkanin wunin ranar suna dafa abinci. A daidai lokacin da za su gama dafa abinci kuma jikinsu ya riga ya gama gajiya, ko sallar Isha'i basa iya zuwa suyi.
5. Sanya buri akan abubuwan da za a ci ko sha
Wasu da yawa suna tunanin cewa azumi ana su mutum ya dinga yawaita ciye-ciye idan ya sha ruwa, hakan ya ke sawa su sanya buri sosai akan abubuwan da zasu ci su sha. Maimakon su mayar da kai akan karatun Al-Qur'ani da sauran ibada wadanda za su kawo wa mutum lada.
KU KARANTA: Jerin abubuwa 20 da basa karya azumi
6. Yawaita bacci
Wasu suna ganin cewa yawaita bacci a yinin da suke azumi ya na sanyawa su samu saukin azumi. Suna tunanin kuma bacci yana nesanta su da aikata wasu ayyuka na haramun. Hakan ba gaskiya bane. Kamata ya yi ku cinye rabin ranar kuna karatun Al-Qur'ani nafiloli da yawaita tuba ga Allah Subhanahu Wa Ta'ala.
7. Bata lokaci wurin ayyukan banza
Duk wani musulmi na kwarai bai kamata ace yana batawa kanshi lokaci ba wurin ayyukan banza. Kamata ya yi mu dage da ibada.
8. Jinkiri wurin buda baki
Akwai wasu a cikinmu wadanda basa shan ruwa har sai an dauki wasu lokuta masu tsawo da kiran sallah. Wasu su na yin hakan ne saboda basa so a gansu su na gaggawa wurin shan ruwa. Addini shine ya nuna cewar ka sha ruwa da wuri, da zarar kaji an kira sallah.
9. Kashe makudan kudade wurin siyan kayan buda baki
Ana so mutum ya kira 'yan uwa musulmi su sha ruwa tare, amma ba ace ya kashe makudan kudade wurin sayen kayan buda baki ba, ko kuma ya mayar da abin kamar wurin biki.
10. Cigaba da aikata ayyukan sabo
Azumi ba wai kawai ance ka kauracewa ci da sha bane, ance mutum ya kauracewa dukkanin wasu ayyukan sabo irinsu karya, rigima, gulma, mugunta, musu, sata da dai sauran manyan laifuka na sabo.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng