An samu gawar wata budurwa da ta fara rubewa a dakin kwanan daliban jami'ar Jos
An samu gawar wata daliba, Mercy Naan, mai shekaru 23, dake shekara ta biyu a bangaren karatun kasuwanci, a dakin kwanan dalibai mai suna 'Zion' a Naraguta.
Tun a ranar 3 ga watan Mayu, iyayen dalibar suka shigar da korafi a ofishin tsaro na jami'ar a kan cewar diyar su ta bata.
Rundunar 'yan sandan jihar Filato, ta bakin kakakinta, DSP Tyopev Terna, ta tabbatar da labarin mutuwar dalibar, ta ce an gano gawar ta ne bayan daliban dake kwana a dakin sun yi korafi da wani wari mai karfin gaske dake fitowa daga dakin dalibar ranar Lahadi.
Rundunar 'yan sandan ta ce liktoci a asibitin jami'ar sun tabbatar da mutuwar ta, sannan an ajiye gawar a dakin ajiya na sashen karatun ilimin sanin sassan jikin bil'adama (Anatomy).
Kazalika ta bayyana cewar ta fara binciken sarkakiyar dake tattare da mutuwar matashiyar dalibar.
Sai dai, da aka tuntubi mataimakin rijistaran jami'ar mai kula da bangaren yada labarai da sadarwa, Abdullahi Abdullahi, ya ce jami'ar na gudanar da bincike domin tabbatar da cewar matashiyar dalibar makarantar ce ta hakika.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace mutum biyu a harin da suka kai gidajen malaman kwalejin kimiyya a Filato
Abdullahi ya kara da cewa da zarar hukumar jami'ar ta kammala bincike tare da samu dukkan bayanan marigayiyar, za a tuntubu iyayenta kafin jami'ar ta fitar da wani jawabi a hukumance.
Ya bayyana cewar matukar ba hakan jami'ar tayi ba, duk wani jawabi za ta dauke shi ne a matsayin hasashe kawai, ya kara da cewa hukumar makarantar da hadin gwuiwar hukumomin tsaro za su gudanar da binciken kwakwaf a kan lamarin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng