Innalillahi wa inna illahi raji’un: Jarumar kannywood Binta Kofar Soro ta rasu

Innalillahi wa inna illahi raji’un: Jarumar kannywood Binta Kofar Soro ta rasu

Allah yayi wa fitacciyar jarumar nan ta dandalin shirya fina-finan Hausa wato Kannywood, Hajiya Binta Kofar Soro rasuwa.

Hajiya Binta, kamar yadda abokanan aikinta ke kiranta da shi, ta rasu ne a ranar Asabar, 4 watan Mayu da safe sannan anyi jana’izan ta a garin Kano.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Jarumi kuma fitaccen dan wasa, Nuhu Abdullahi ne ya tabbatar mata da labarin rasuwar Binta.

”Lallai Hajiya Binta ta rigamu gidan gaskiya a yau Asabar. Farfajiyar fina-finai na Kannywood ta yi rashi matuka domin ba a wasa ba ma kawai Hajiya Binta uwace garemu ba ki daya."

Innalillahi wa inna illahi raji’un: Jarumar kannywood Binta Kofar Soro ta rasu
Innalillahi wa inna illahi raji’un: Jarumar kannywood Binta Kofar Soro ta rasu
Asali: UGC

Haka zalika manyan jarumai kamar su Halima Atete, Ali Nuhu, Rahama Sadau, Sani Danja, Aisha Humairah da dai sauran abokanan aikin ta duk sun bi marigayiyar da addu’o’in Allah ya sa ta huta a shafukansu na zumunta ta Instagram.

Wasu da dama ma sun canja hotunan su zuwa hoton marigayiyar.

Lokuta da dama dai Hajiya Binta kan fito a matsayin uwa a cikin shirin fina-finan Kannywood, kuma ma a kwanankin bayan nan ne tayi bikin yarta wanda ya samu halartan abokan sana’arta da dama.

KU KARANTA KUMA: Wani likita ya makala wa yara 65, da manya 25 cutar kanjamau

Wani abun al’ajabi da yasa mutane jimami shine kwanaki biyu da suka abata, jarumar ta wallafa wani rubutu a shafintana Instagram inda take neman yafiyar al’umma wanda tayi wa laifi da wadanda ma bata yiwa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng