Wata 'yar Najeriya ta yi kokarin harbe wani dan sanda da ya kamata da kwaya a kasar Italy

Wata 'yar Najeriya ta yi kokarin harbe wani dan sanda da ya kamata da kwaya a kasar Italy

- Wata 'yar Najeriya da 'yan sanda suka kama a kasar Italy da miyagun kwayoyi ta yi kokarin halaka daya daga cikin 'yan sandan da suka kamata

- Budurwar ta yi yunkurin harbe dan sandan yayin da ta warce bindigar shi daga jikin shi

An kama wata budurwa mai suna Blessing Rapuruchukwu Okafor, mai shekaru 31 a duniya da miyagun kwayoyi a filin tashi da saukar jiragen sama na Trevisto, da ke kasar Italy.

Rahotanni sun nuna cewa Blessing ta na daya daga cikin 'yan gudun hijira wadanda suka shiga kasar Italy din ta kasar Libya, inda ake tsallakawa da su ta ga cikin teku a jirgin ruwa. Jami'an tsaron kasar sun dauki Blessing zuwa asibiti domin bincike akan kwayoyin da ta hadiye a cikinta.

Wata 'yar Najeriya ta yi kokarin harbe wani dan sanda da ya kamata da kwaya a kasar Italy
Wata 'yar Najeriya ta yi kokarin harbe wani dan sanda da ya kamata da kwaya a kasar Italy
Source: Facebook

Bayan zuwan na su asibitin sai aka kai ta bandaki domin ta amayo da kwayar da ke cikin na ta, sai dai kuma Blessing ta yi kokarin kashe jami'in dan sandan da ya raka ta bandakin, domin ya kula da ita.

A cewar jami'in dan sandan, wacce ake zargin ta kwace bindigar da ke jikin shi, inda ta yi kokarin harbin shi da ita, sai dai kuma cikin rashin sa'a ba ta san cewa bindigar a kulle ta ke ba, inda ta dinga harbawa amma ta ki tashi.

KU KARANTA: Kasashe 37 da suke biyan albashi mafi yawa a 2019

A lokacin ne shi kuma jami'in dan sandan da taimakon 'yan uwansa 'yan sanda suka yi kokari wurin kwace bindigar daga hannun wacce ake zargin.

A cikin wannan makon ne, aka kama wata budurwa mai suna Zainab Aliyu a kasar Saudiyya da kwaya a cikin jakarta, sai dai kuma gwamnatin tarayyar kasar nan ta sanya baki a lamarin, inda aka samu damar ceto ranta daga hannun hukumomin kasar ta Saudiyya, wanda suke yankewa duk wani mutumi da suka samu da kwaya hukuncin kisa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel