'Yan bindigan da suka sace Magajin Garin Daura sun tuntubi iyalansa

'Yan bindigan da suka sace Magajin Garin Daura sun tuntubi iyalansa

Masu garkuwa da mutane da suka sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba sun tuntubi iyalansa bayan wasu awanni da sace shi kamar yadda Daily Trust ta gano daga wata kwakwarar majiya a jiya Alhamis.

'Yan bindigan sun sace babban basaraken masarautar Dauran ne a gaban gidansa da ke garin na Daura mai dimbin tarihi jim kadan bayan kammala salar Magariba a ranar Laraba.

"Wadanda suka sace Magajin Garin sun kashe wayoyin sa na salula bayan sunyi awon gaba da shi amma daga bisani sun bashi damar yin magana da iyalansa a takaice," inji wani na kusa da iyalan basaraken.

"Magajin Garin ya tabbatarwa iyalansa cewa yana hannun masu garkuwa da mutane ne."

'Yan bindigan da suka sace Magajin Garin Daura sun tuntubi iyalansa

'Yan bindigan da suka sace Magajin Garin Daura sun tuntubi iyalansa
Source: UGC

DUBA WANNAN: Bayan cin zabe a PDP, shugaban marasa rinjaye ya koma APC

Shi dai Magajin gari shahararren attajiri ne daya taba kasancewa kwanturola a hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, watau kwastam, kanin Sarkin Daura ne, surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne sakamakon yana auren Hajiya Bilki, diyar yayar Buhari Hjiyar Rakiya, sa’annan diyarsa Fatima na auren babban dogarin Buhari, Kanal Mohammed Abubakar.

A baya, majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu shaidun gani da ido sun bayyana yadda lamarin ya auku, tun daga tsayuwar yan bindigan a kofar gidan Magaji, fitowarsu daga mota, zuwa daukeshi, har zuwa yadda suka yi awon gaba dashi.

Wani da abin ya faru a gabanshi, Malam Abdullahi yace “A cikin motoci biyu suka zo, Toyota Hilux da wata Pijo 406, sun tarar da Magaji a gaban gidansa dake kwanar Agam tare da jama’a bayan munyi sallar Magariba, kai tsaye suka yi kansa, yayin da guda ya dinga harbi a sama, da haka suka tursasa mai shiga motar, suka arce dashi.”

Sai dai jama’ da dama sun shaida cewa Magajin gari baya komawa cikin gida bayan sallar magariba, don haka yake zama a kofar gidansa tare da jama’ansa har sai sun yi sallar Isha’I, wannan ya baiwa yan bindigan daman samunsa cikin sauki.

Wani makwabcin Magaji, mai suna Malam Muhammad ya bayyana cewa “Kafin zuwan barayin, an jiyo Magaji yanata amsa waya, da alama wasu mutane sun fada masa suna hanyar zuwa ganinsa a gida, ai kuwa zuwansu keda wuya suka kamashi suka shigar cikin mota suka tsere.”

Duk da cewa jama’a sun razana, amma wasu sunyi karfin halin kokarin kubutar da Magajin gari, amma sai guda daga cikin yan bindigan ya bude wuta a sama, daga nan kowa yayi ta kansa, sai dai an tabbatar hanyar Zangon Daura suka bi dashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel