Jirgin yakin Isra'ila ya kai mummunan hari zirin Gaza
- Wasu jiragen yakin kasar Isra'ila sun kai wani mummunan hari kan sansanin sojojin Hamas da ke arewacin Gaza
- Kasar Isra'ila ta ce ba za ta saurarawa duk kasar da za ta yi yunkurin kawo ma al'ummar ta hari ba
A yau Alhamis dinnan ne 2 ga watan Mayu, 2019, jirgin saman yakin kasar Isra'ila ya kai wani mummunan hari kan dakarun Hamas a arewacin Gaza.
Sojojin Isra'ilan sun bayyana cewa sun kai harin ne bayan da wata wuta ta kama a daji kusa da Eshkol da ke yankin kudancin Isra'ila.
Rahotanni sun nuna cewa wutar ta kama ne saboda wani abun fashewa da ya fashe a kusa da wani birni na kasar Isra'ila.
Wasu shaidu 'yan kasar Palasdinu sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai cewa jirgin saman ya kai harin kan wani yanki na sansanin sojojin Hamas a arewacin Gaza.
KU KARANTA: Masu garkuwa da mutaane sun bayyana dalilan da yasa suke satar mutane a kasar nan
Rahotanni sun nuna cewa, ba ayi asarar rai ba, amma an bata abubuwa da dama a sansanin sojojin.
"Sojojin Isra'ila za su cigaba da kashe duk wasu mutane da suka yi yunkurin cutar da al'ummar kasar Isra'ila," in ji rahoton.
An kwashe shekaru masu yawan gaske ana samun hare-hare a yankin zirin Gaza.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng