Yadda za’a magance matsalar ‘yan Najeriya masu tsallakawa zuwa kasashen wajen, inji jakadan Switzerland

Yadda za’a magance matsalar ‘yan Najeriya masu tsallakawa zuwa kasashen wajen, inji jakadan Switzerland

-Yawancin matasa na bari Najeriya ne domin neman aikinyi a kasashen waje

-Da dama daga cikinsu basu bin hanyar da ta dace, sai dai haramtacciyar hanya

Babban kwamishinan kasar Switzerland wanda ya ziyarci Najeriya mai suna Walter Leimgruber shine yayi wannan jan hankalin ranar Alhamis yayinda yake tattaunawa da gwamnatin Najeriya akan yadda za’a karfafa matasan Najeriya.

Leimgruber ya shaidawa manema labarai a jihar Legas cewa ayyukan more rayuwa da kuma samr da aikin yi ga matasa zai dauke masu hankali ya kuma hanasu fita zuwa kasar Switzerland wanda yawanci keyi ta haramtacciyar hanya.

Yadda za’a magance matsalar ‘yan Najeriya masu tsallakawa zuwa kasashen wajen, inji jakadan Switzerland
Yadda za’a magance matsalar ‘yan Najeriya masu tsallakawa zuwa kasashen wajen, inji jakadan Switzerland
Asali: UGC

KU KARANTA:Gwamnatin Kebbi bata da matsaya akan biyan mafi karancin albashin N30,000

“ Akasarin matasan Najeriya na kallon kasar Switzerland ne a matsayin kasar dake da dimbin arziki kana kuma idan sun je can zasu samu aikinyi wanda za’a biyasu da tsoka.

“ Sai dai basu duba wahalar samun wadannan abubuwa, tabbas ba’a samun hakan cikin sauki. Gwamnatin Najeriya dama yan kasuwa yakamata su kirkiro hanyoyin sana’o’i da kuma ayyuka domin matsansu domin yin hakan shine kawai zai sa su zauna gida." Inji kwamishinan.

Kwamishinan yace sun zo Najeriya domin tattauna al’amuran da suka shafi hijirar yan Najeriya zuwa kasar Switzerland. Akwai bukatar mu hada hannu da kungiyoyi kamar International Organization for Migration (IOM), UNHCR da kuma sauran kasashen da masu hijirar suka fito.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel