N-Power na gargadi ga al'umma akan 'yan damfara

N-Power na gargadi ga al'umma akan 'yan damfara

-Yan damfara na amfani da bayanan bogi suna yadawa a shafukan sada zumunta akan cewa N-Power ta fara daukar ma'aikata

- N-Power ta fito ta karyata wannan labarin kanzon kuregen, ta ce mutane su daina saka bayanan su a shafukan saboda gudun fadawa tarkon 'yan damfarar

Shirin N-Power na gwamnatin tarayya ya gargadi daukacin al'ummar Najeriya cewa ba su fara daukar sababbin ma'aikata ba a yanzu.

An bayyana hakan ne, bayan samun wasu labarai na bogi da ke yawo a kafar sada zumunta na zamani da ke nuna cewa ma'aikatar ta N-Power ta fara daukar ma'aikata, ma'aikatar ta karyata wannan labari inda ta bayyana cewa labari ne na 'yan damfara masu son amfani da bayanan mutane.

N-Power na gargadi ga al'umma akan 'yan damfara

N-Power na gargadi ga al'umma akan 'yan damfara
Source: Twitter

"N-Power ba su fara daukar ma'aikata ba. Saboda haka ku dai na saka bayanan ku cikin shafin yanar gizo na 'yan damfara. Idan muka fara daukar ma'aikatan, za mu sanar da kowa da kowa a kasar nan," ma'aikatar ta yi wannan gargadi.

A watan Afrilun da ya gabata ne, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wa 'yan Najeriya alkawarin cewa, gwamnatin tarayya za ta fadada shirin N-Power.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutaane sun bayyana dalilan da yasa suke satar mutane a kasar nan

Osinbajo ya yi alkawarin ne a ranar 29 ga watan Maris a lokacin taron murnar cikar Bola Tinubu shekaru 67 a duniya.

Mataimakin shugaban kasar kuma ya yi alkawarin cewar gwamnatin da za a shiga karo na biyu, za ta zamto mai ban sha'awa ga kowanne dan Najeriya, duk da dai cewa za a fuskanci kananan kalubale.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel