Amarya ta haihu a daidai lokacin da ake daura mata aure

Amarya ta haihu a daidai lokacin da ake daura mata aure

- Wani abu da wasu suka misalta shi da baiwa da kuma abun al'ajabi ya faru da wata mata a Najeriya, inda ta haihu a dai dai lokacin da ake daura mata aure ita da masoyinta

- Lamarin ya kawo cece-kuce a shafukan sada zumunta na zamani, inda wasu ke ganin lamarin bashi da alaka da wata baiwa ko abin al'ajabi

Wata mata a Najeriya ta haihu a ranar da ake daura aurenta ita da masoyinta.

A cewar wata mata mai suna Cynthia Chidimma Ezike, wacce ta sanya labarin a shafinta na sada zumunta na Facebook, ta ce Amaryar da ta haihu din matar dan uwanta ce.

Amarya ta haihu a daidai lokacin da ake daura mata aure
Amarya ta haihu a daidai lokacin da ake daura mata aure
Source: Facebook

Ga abinda matar ta ce a shafin na ta:

"Mun godewa Allah mai girma da irin wannan baiwa da ya yi mana, matar dan uwana ta haifi jariri a dai dai lokacin da ake daura aurenta, kuma ranar ce nima nake murnar ranar haihuwata, saboda haka muna godewa Allah da irin wannan baiwa da ya yi mana."

KU KARANTA: An kama saurayin nan da ya kashe 'yan uwan budurwarshi su 8 saboda ta ce bata son shi

Wannan labari dai ya kawo kace nace sosai a shafin sada zumunta na Facebook, musamman ma da ya ke ba kasafai aka fiya samun irin wannan labaran ba.

Wasu mutanen suna ganin hakan ba baiwa ba ce, domin babu yadda za ayi mace ta haihu ba tare da miji ba. Wasu da yawa ma sun fara zargin mata da mijin ko suna da wata alaka kafin a zo mawar yin auren na su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel