El Zakzaky da Matar sa na bukatar a duba lafiyar su cikin gaggawa a kasar waje - Likitoci

El Zakzaky da Matar sa na bukatar a duba lafiyar su cikin gaggawa a kasar waje - Likitoci

Kwararrun likitoci da suka gudanar da bincike kan koshin lafiyar shugaban kungiyar masu akidar Shi'a na Najeriya, Sheikh Ibrahim El- Zakzaky da kuma mai dakin sa Zeenatu, sun nemi a yi gaggawar fidda su kasar waje domin samun ingatacciyar kulawa ta nema masu magani.

Kungiyar kwararrun liktocin daga kasar Birtaniya da ta ziyarci El Zakzaky da ke tsare a hannun hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS, ta hadar da likitan ido, likitan zuciya da kuma kwararren likitan 'kashi.

Sheikh Ibrahim El Zakzaky

Sheikh Ibrahim El Zakzaky
Source: Twitter

Yayin ganawar sa da manema labarai, jagoran tawagar likitocin, Dakta Kazim Akber Dhalla da ya kasance likitan idanu, ya ce duba da binciken koshin lafiya da suka gudanar a kan Sheikh Zakzaky da kuma mai dakin sa, akwai muhimmiyar bukata ta fidda su kasar waje domin ba su cikakkiyar kulawa da ingatattun magunguna.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sheikh Zakzaky ya rasa idon sa guda yayin harin daukar fansa cikin fushi da hukumar dakarun sojin kasa ta kai gidan sa da ke garin Zariya tun a shekarar 2015 da ta gabata.

KARANTA KUMA: Karuwanci babban zunubi ne a koyarwar addinin Islama da na Kirista - Abayomi Shogunle

Kazalika a yayin harin azal ta afkawa ma dakin sa wadda ta samu munanan raunuka gami da mabiyan sa kimanin 340 da su ka hadar da 'ya'yan sa uku da suka riga mu gidan gaskiya.

A halin yanzu El-Zakzaky, mai dakin sa da kuma mabiyan sa da dama da ke tsare na ci gaba da bai wa duga-dugan su hutu a hannun hukumar DSS.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel