Sojoji 5 sun halaka, an nemi 30 an rasa yayin artabu da mayakan Boko Haram

Sojoji 5 sun halaka, an nemi 30 an rasa yayin artabu da mayakan Boko Haram

Kimanin rayukan dakarun sojojin Najeriya biyar sun salwanta yayin da aka nemi sojoji 30 aka rasa biyo bayan wani mummunan hari da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta kai kan wani sansanin dakaru da ke jihar Borno.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, mayakan boko haram tare da hadin gwiwar kungiyar ta'adda ta ISIS, sun yiwa dakarun sojin Najeriya diban karan mahaukaciya a ranar Juma'ar cikin jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sojoji 5 sun halaka, an nemi 30 an rasa yayin artabu da mayakan Boko Haram

Sojoji 5 sun halaka, an nemi 30 an rasa yayin artabu da mayakan Boko Haram
Source: Facebook

Majiyar rahoton ta shaidawa manema labarai na jaridar AFP cewa, a halin yanzu an tsinto gawawwakin sojoji biyar da rayukan su suka salwanta a yayin kare martabar kasa yayin da ake ci gaba da laluben dakaru kimanin 30 da kawowa yanzu an rasa su.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, ayarin mayakan Boko Haram haye kan motocin yaki da kuma babura dauke da makamai na kare dangi, sun kai hari kan sansanin dakarun soji da ke mararrabar Kimba kilomita 135 zuwa birnin Maiduguri.

KARANTA KUMA: Gobara ta kone muhallai 140 a sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno

Cikin makonni kadan da suka gabata, dakarun hadin gwiwa na sojojin Najeria, Kamaru da kasar Chadi, na ci gaba da yiwa mayakan Boko Haram tarnaki a maboyan su da ke gabar tafkin Chadi.

Rayukan dubunnan mutane sun salwanta yayin da miliyoyi da dama suka rasa muhallan su tun yayin da kungiyar mayakan boko haram ta daura damarar ta'addanci a kasar nan da wasu kasashe na yankin Afirka ta Kudu tsawon shekaru goma da suka gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel