Saurayi ya haye saman bishiya ba zai sauko ba sai an bashi Matar aure a Yobe (Hoto)

Saurayi ya haye saman bishiya ba zai sauko ba sai an bashi Matar aure a Yobe (Hoto)

Kai jama’a, abin mamaki baya karewa a duniyar nan, gaskiya ne da guk wanda keda rai, zai sha kallo, kamar yadda ta faru a jahar Yobe dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya, inda soyayya ta tunzura wani saurayi yayi abin al’ajabi.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Saifullahi A Sale ne ya bada wannan labari, tare da daura hoton wani saurayi daya hau kololuwar bishiyar tsamiya saboda tsananin soyayyar da yake yi ma budurwarsa.

KU KARANTA: Yansanda sun kama mutumin daya kashe wani babban basaraken jahar Kaduna

Saurayi ya haye saman bishiya ba zai sauko ba sai an bashi Matar aure a Yobe (Hoto)
Saurayi ya haye saman bishiya ba zai sauko ba sai an bashi Matar aure a Yobe
Source: Facebook

Dayake ruwa baya tsami banza, majiyar Legit.ng ta ruwaito ba haka nan wannan matashi yayi dare dare a saman bishiyar tsamiyar ba, a’a, asali ma bishiyar tsamiyar a kofar gidansu budurwar tasa take.

Rahotanni sun tabbatar da cewar shaukin soyayya ne ta kama wannan matashi, don haka ya haye saman bishiyar da nufin ba zai sauko ba har sai mahaifin budurwar ya fito ya bayyana masa amincewarsa na bashi aurenta a fili.

Shi dai wannan matashi da bamu samu takamaimen sunansa ba ya dauki alwashin ba zai sauko daga saman bishiyar ba idan har mahaifin budurwar da yake tsakanin kauna bai bashi tabbacin zai bashi aurenta ba.

Toh fa, soyayya aka ce gamon jini ce, amma fa idan da kauna, wannan lamari ba shine farau ba a harkar soyayya, amma dai shima yana dauke da wani nau’i irin na ban mamaki, idan zaku tuna a makon data gabata mun kawo makamancin wannan rahoto.

Inda a jahar Bayelsa wani saurayi ya kashe kansa sakamakon yar karamar sabani daya samu da budurwarsa, bayan ta bayyana masa cewa zata koma garinsu, shi kuma ya bata hakuri har ta hakura, amma kwatsam a ranar bikin Easter ta nemi yazo suje yawon shakatawa, yaki ya, dawowarta keda wuya ta tarar ya kashe kansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel