Hukumar EFCC ta shigar da karar Bala Mohammed a gaban Kotu
Yayin da ake saura wata guda cak a rantsar da sababbin gwamnoni da shugaban kasa a Najeriya, EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa tana neman kama Bala Mohammed.
Kamar yadda labari ya samu zuwa mana, A yau Litinin, 29 ga Watan Mayu ne Sanata Bala Mohammed na jam’iyyar PDP, zai bayyana a gaban kotu, inda hukumar EFCC ta ke zargin sa da wasu manyan laifuffuka har 6.
Hukumar EFCC tana tuhumar gwamnan mai-jiran gado da laifin kin bayyana kadarorinsa, da kuma ba hukuma bayanan karya a game da dukiyar da ya mallaka. Haka kuma ana zargin Bala Mohammed da karbar cin hanci.
Za a gurfanar da Kauran Bauchi ne a babban kotun tarayya da ke Maitama a cikin Garin Abuja, inda zai amsa laifuffuka har 6. Wahab Shittu shi ne Lauyan da EFCC ta sa domin ya binciki gwamnan na jihar Bauchi mai jiran-gado.
KU KARANTA: Atiku ya hango nasara a shari’ar zaben 2019 da yake yi da Buhari
Bala Mohammed ya bayyana cewa ba komai bane wannan illa cinne ne gwamnatin APC ta ke yi masa, bayan ganin ya doke gwamnan ta a zaben 2019. Mohammed yace ba yau aka saba bincikensa ba, kuma ba ya jin tsoron komai.
Wanda ake tuhuma ya sha alwashin kare kan sa a gaban kotu kamar yadda ya samu nasara shari’ar sa da gwamnatin tarayya kwanaki. Bala Mohammed dai ya rantse sai ya binciki gwamnatin APC idan ya hau mulki a jihar Bauchi.
Tsohon Ministan na babban birnin tarayya Abuja, Sanata Bala Mohammed, ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi da aka yi a watan jiya inda ya doke gwamna mai-ci Mohammed Abubakar na jam’iyyar APC.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng