Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi (Hotuna)

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi (Hotuna)

A ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu, dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben da aka kammala, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), ya kai wa babban shehun darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ziyara a gidansa dake Kano.

Dan takarar ya samu rakiyar dan takarar mataimakinsa, Kwamred Aminu Abdulsalam, tare da wasu magoya baya da masoyan sa.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta nemi kotun da ke sauraron karar zaben 2019 a jihar Kano, da ta bayyana cewa ita ce ta lashe zaben gwamna da aka yi a maimakon Abdullahi Umar Ganduje.

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi (Hotuna)

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi
Source: Facebook

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi (Hotuna)

Abba Gida-Gida a gidan Dahiru Dahiru Bauchi
Source: Facebook

Jam’iyyar tana nema kotu ta soke nasarar da gwamna mai-ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC mai mulki ya samu a zaben na bana.

DUBA WANNAN: Saraki ya samu sabon aiki a hukumar kasa da kasa ta IHRC

PDP tana so ne a ba ‘dan takararta, Injiniya Abba K. Yusuf nasara a zaben na 2019. Lauyoyin PDP sun fadawa kotun karar zaben cewa ‘dan takarar ta na 2019, Abba Kabiru Yusuf, ya samu kuri’un da ake nema wajen lashe zaben gwamna don haka ta nemi a bayyana shi a matsayin zababben gwamna na jihar Kano.

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi (Hotuna)

Abba Gida-Gida a gidan Dahiru Dahiru Bauchi
Source: Facebook

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi (Hotuna)

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Bauchi
Source: Facebook

A karar da PDP ta maka a gaban kotun mai sauraron korafin zabe mai shafi 1685. Jam’iyyar hamayyar tana ja da soke zaben wasu yankuna a cikin karamar hukumar Nasarawa da hukumar zabe mai zaman kan-ta tayi a watan jiya.

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi (Hotuna)

Abba Gida-Gida da Dahiru Bauchi
Source: Twitter

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi (Hotuna)

Abba Gida-Gida a gidan Dahiru Bauchi
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel