Ronaldo ya ci kwallo ta 600 a fagen kungiyoyin kwallon kafa

Ronaldo ya ci kwallo ta 600 a fagen kungiyoyin kwallon kafa

Yayin wani wasa da aka tashi kunnen doki tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan da Juventus a gasar Serie A ta kasar Italiya, fitaccen dan wasa Cristiano Ronaldo, ya zura kwallo ta 600 cikin koma a fagen kwallon kafa ta kungiya.

Wasan gasar kofin Serie A da aka tashi 1-1 a ranar Asabar, Ronaldo ya jefa wa kungiyar sa ta Juventus kwallo daya tilo da ta tsamo su daga shan kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan.

Ronaldo ya ci kwallo ta 600 a fagen kungiyoyin kwallon kafa

Ronaldo ya ci kwallo ta 600 a fagen kungiyoyin kwallon kafa
Source: Getty Images

Kamar dai yadda ya saba, Ronaldo ya fidda kungiyar sa kunya a minti na 62 bayan da dan wasan kungiyar Inter Milan Radja Nainggolan, ya yi masu shigar wuri tun a minti na 7 da sai mai tsaron raga na kungiyar Juventus, Woljciech Szczesny ya ji ana yi.

Yayin da Ronaldo mai shekaru 34 a duniya ya jefa wa kungiyar Juventus kwallaye 27 a bana, ya zura kwallaye 450 a tsohuwar kungiyar sa ta Real Madrid, 118 a Manchester United da kuma kwallaye biyar a kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lisbon.

KARANTA KUMA: Cikin shekaru hudu an sace Shanu 74,000 a jihar Kaduna

Kwallon da Ronalda ya jefa a jiya Asabar, 27 ga watan Afrilun 2019, ta kasance kwallo ta 600 da ya zura cikin koma a kungiyoyin kwallon kafa 4 da ya yiwa hidima a tarihin rayuwar sa. Duniya ta dauka kuma yawu ya gudana kan harsunan al'umma domin kwarara yabo a kan Ronaldo.

Tun a makon da ya gabata kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta lashe gasar kofin Serie A na bana yayin da ya rage sauran wasanni 4 a karkare gasar a wannan shekara. Kungiyar ta lashe gasar sau takwas kenan a jere ba bu wanda ya iya lakace ma ta hanci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel