Cikin shekaru hudu an sace Shanu 74,000 a jihar Kaduna

Cikin shekaru hudu an sace Shanu 74,000 a jihar Kaduna

Mai nadin sarautar gargajiya ta garin Kujama da ke karkashin karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna, Alhaji Idris Gunderi, ya ce Barayi sun yi awon gaba da fiye da shanu 74,000 cikin tsawon shekaru hudu da suka gabata a fadin jihar Kaduna.

Cikin shekaru hudu an sace Shanu 74,000 a jihar Kaduna

Cikin shekaru hudu an sace Shanu 74,000 a jihar Kaduna
Source: UGC

Ya ce kawowa yanzu ba bu wani tallafi na agaji da mamallakan shanun suka samu daga bangaren gwamnatin jiha ko kuma ta tarayya domin saukaka masu radadin halin kaka-nika-yi da suka afka kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jagoran rigar Fulani da ke garin Kujama yayin amsa tambayoyin manema labarai a birnin Kaduna ya ce, ya na da cikakken jerin sunayen wadanda wannan annoba ta satar shanu ta shafa.

Yayin cewa ba bu ko mudun Masara na tallafi da suka samu, ya nemi gwamnatin tarayya da kuma ta jihar Kaduna a kan yi masu yayyafin agaji domin saukaka radadin halin ni 'ya su da sace dukiyar su ta jefa su ciki.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan Fashi da Makami 4 a jihar Neja

Ya bayyana takaicin sa dangane da yadda annobar satar shanu ke ci gaba da kasancewa ruwan dare tare da kamari ba tare da wani yunkurin kawo karshen sa ba daga bangaren hukomomin tsaro masu ruwa da tsaki.

Cikin taushin murya da neman jin kai, Alhaji Gunderi ya bayyana yadda Fulani a halin yanzu su shiga cikin hali na tagayyara a yayin fafutikar ciyar da iyalan su a sanadiyar rashin dabbobi na kiwo da barayi su ka yi awon gaba da su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel