Yanzu-yanzu: An sace wasu 'yan China a Najeriya

Yanzu-yanzu: An sace wasu 'yan China a Najeriya

- Wasu masu garkuwa da mutane sun sace wasu 'yan kasar China da suke aikin gina hanya a jihar Ebonyi

- Barayin sun sace mutanen biyu sun shiga daji da su har yanzu ba a san inda suke ba

Wasu masu garkuwa da mutane sun sace wasu 'yan kasar China guda biyu, Sun Zhixin da Quing Hu, a jihar Ebonyi, yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Mutanen biyu suna aiki ne da kamfanin gine gine na Tongyi.

An sace su aa dai dai lokacin da suke aikin hanyar karamar hukumar Ohaozara ta jihar Ebonyi, inda barayin suka dauke su ta karfin tsiya suka gudu da su.

Yanzu-yanzu: An sace wasu 'yan China a Najeriya
Yanzu-yanzu: An sace wasu 'yan China a Najeriya
Asali: Twitter

An sace su daga wurin aikin da misalin karfe 3:30 na yamma, ranar Larabar nan, yayin da barayin suka zo wurin fuskarsu a rufe.

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa, 'yan China din suna wani wuri da ake kira da Ivo river, lokacin da 'yan bindigar suka zo wurin da makamai, suka tilasta ma'aikatan barin wurin aikin, inda suka dauki 'yan China din suka gudu da su wani wuri da har yanzu an kasa ganowa.

KU KARANTA: Hotuna: Yanzun nan shugaba Buhari ya isa jihar Borno

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Odah Loveth, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce yanzu haka hukumar 'yan sanda ta tura jami'anta domin ceto wadanda aka sace din.

Kwamishinar 'yan ta jihar ta neman mutane su taimakawa hukumar 'yan sanda da bayani domin taimaka musu a binciken su.

Ta kuma nuna damuwarta akan yadda aka yi kamfanin ya fara aiki a irin wannan wurin ba tare da ya nemi taimakon hukumar tsaro ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng