Shugaba Muhammadu Buhari ya bude Makaranta da gidaje a Jihar Borno

Shugaba Muhammadu Buhari ya bude Makaranta da gidaje a Jihar Borno

- Shugaba Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka a Garin Maiduguri

- Gwamnatin Jihar Borno ta gina wasu gidaje da makarantu a jihar

Shugaba Muhammadu Buhari ya bude Makaranta da gidaje a Jihar Borno

Muhammadu Buhari yayin da ya bude wata Makaranta a Maiduguri
Source: Facebook

Dazu nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Borno inda ya kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin Gwamna Kashim Shettima yayi. Jama’a da dama sun yabawa kokarin wannan gwamna.

Daga cikin ayyukan da shugaban kasar ya kaddamar akwai wasu tarin gidaje har 246 da gwamnatin jihar Borno ta gina. An gina wadannan katafaren gidaje masu ban sha’awa ne a cikin babban birnin jihar Borno na Maiduguri.

KU KARANTA: Gwamnan APC yana neman Kotun zabe ta karbo masa nasara a hannun PDP

Shugaba Muhammadu Buhari ya bude Makaranta da gidaje a Jihar Borno

Hotunan gidajen da Shugaba Buhari ya bude a Borno
Source: Facebook

Haka zalika, mai girma gwamna Kashim Shettima mai shirin barin-gado, ya kuma gina wata makarantar firamare mai ban-kayi duk a cikin Garin na Maiduguri. An sanyawa wannan makaranta sunan Babagana Kingibe.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bude Makaranta da gidaje a Jihar Borno

Makarantar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar Borno
Source: Twitter

Gwamnatin Borno ta zabi ta karrama Babagana Kingibe wanda yana cikin manyan ‘yan siyasar jihar. Ambasada Kingimbe ya taba rike mukamin Minista a lokacin Abacha, sannan kuma ya rike Sakataren gwamnatin kasa a 2007.

Wani daga cikin Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai sunaBashir Ahmaad, ya dauki wannan hotuna masu ban sha’awa dazu da rana. Bayan ziyarar Borno, shugaban kasar ya lula zuwa kasar Ingila domin ya huta.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bude Makaranta da gidaje a Jihar Borno

Hoton gidajen da Buhari ya kaddamar a Maiduguri
Source: Twitter

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel