Buratai ya kaddamar da sabon katafaren ginin makaranta a hedikwatar soji a Jaji (Hotuna)
Shugaban rundunar soji ta kasa, Laftanal Janar TY Buratai, ya bude sabon katafaren ginin makarantar sojojin 'infantry' da aka yi a cikin hedikwatar soji ta Jaji da ke jihar Kaduna.
Buratai da ragwar manyan hafsoshin rundunar sojin kasa na jihar Kaduna domin halartar wani muhimmin taro da za a yi a cikin satin nan.
Kafin ya wuce zuwa Jaji domin kaddamar da sabon ginin na zamani, Legit.ng ta kawo muku labarin cewar tawagar shugabannin rundunar soji a karkashin jagorancin shugaban rundunar soji ta kasa, Laftanal Janar TY Buratai, sun ziyarci fadar gwamnatin jihar Kaduna da safiyar ranar Laraba.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Barnabas Bala Bantex, ne ya karbi Buratai da ragowar shugabannin rundunar sojin.
DUBA WANNAN: Maigadi ya zabi a gina tuka-tuka a kauyensu a kan karbar kyautar gida
A jawabin mataimakin gwamnan, ya gode wa rundunar soji a kan kafa sansani a Kafanchan da Birnin Gwari.
A nasa jawabin, Buratai ya shaida wa mataimakin gwamnan cewar zasu daga darajar sansanin biyu zuwa manyan rundunar sojoji.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng