Wani yaro ya mutu yayin da yaje wanka kogi a jihar Kano

Wani yaro ya mutu yayin da yaje wanka kogi a jihar Kano

- Wani yaro ya nutse a ruwan wani kogi a jihar Kano yayin da ya je yin wanka

- Yaron mai shekaru goma a duniya an hango gawarshi ta na yawo a kan ruwa

- Hukumar 'yan sanda ta gargadi al'umma da su hana yaransu zuwa wanka kogi musamman a wannan lokacin na zafi

Wani yaro dan shekara goma a duniya, mai suna Shu'aibu Musa, ya mutu a ruwa yayin da yaje yin wanka a wani kogi mai suna "Ramin Tasiu" a hanyar Sheika da ke karamar hukumar Kumbotso cikin jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Mista Sa'idu Mohammed, shine ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya da ke jihar Kano a yau Larabar nan, inda ya ke cewa lamarin ya faru jiya Talata da rana a lokacin da marigayin ya tafi yin wanka a kogin.

Wani yaro ya mutu yayin da yaje wanka kogi a jihar Kano

Wani yaro ya mutu yayin da yaje wanka kogi a jihar Kano
Source: Depositphotos

"Mun samu kiran waya daga wani mutumi mai suna Malam Abdullahi Naguru da misalin karfe 3:15 na yamma, inda ya ke bayyana mana cewa sun gano gawar Musa ta na yawo a kan ruwa.

"Muna samun rahoton muka tura jami'anmu wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 3:30, domin kai dauki ga yaron.

"Mun samu gawar Musa a kwance, inda muka mika shi ga mahaifinsa Alhaji Musa Ya'u, domin yi mishi jana'iza a kai shi makwancinsa," in ji shi.

KU KARANTA: Zamfara: Rundunar sojin sama ta yiwa 'yan bindigar jihar Zamfara luguden wuta

Mohammed ya shawarci jama'a musamman ma iyaye da masu unguwanni akan su hana 'ya'yansu zuwa kogi wanka, domin gujewa irin wannan lamarin a nan gaba.

Ba wannan ne karo na farko da irin wannan lamarin ya faru a jihar ta Kano ba, musamman a lokacin zafi da yara ke nemawa kansu sauki wurin zuwa wanka a kogi

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel