ISIS ta bayyana hotunan wadanda suka kai harin Sri Lanka daya kashe mutane 321

ISIS ta bayyana hotunan wadanda suka kai harin Sri Lanka daya kashe mutane 321

Fitacciyar kungiyar ta’addancin nan ta Duniya, watau ISIS, ta dauki nauyin alhakin kai mummunan harin daya auku a kasar Sri Lanka a ranar Lahadin data gabata a kasar Sri Lanka, tare da bayyana hotunan fuskokin yan ta’addanta da suka kai harin.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ISI ta sanar da haka ne ta gidan talabijin dinta na Amaq, inda aka hangi dan ta’addan nan mai suna Zahran Hashim a gaba gaba, yayin da sauran yan ta’adda ke take masa baya fuskokinsu a rufe.

KU KARANTA: Alkali ya daure wasu Matan Musulmai 2 da suka yi shigar banza a garin Kaduna

ISIS ta bayyana hotunan wadanda suka kai harin Sri Lankk daya kashe mutane 321
Yan ta'addan
Asali: UGC

Sai dai kungiyar ta bayyana sunayen sauran yan ta’addan da suka kitsa wannan hari kamar haka; Abu Ubayda, Abu Khalil, Abu Al-Mukhtar, Abu Al-Bara’a, Abu Muhammad da kuma Abu Abdullah, kuma dukkansu sun bayyana mika mubaya’ansu ga ISIS.

“Wadanda suka shirya wannan hari daya kashe mutanen kasashen hadin gwiwa da kuma kiristoci a kasar Sri Lanka yan kungiyar ISIS ne.” Inji ISIS, sai dai hukumomin kasar Sri Lanka suna zargin wasu kungiyoyin ta’addanci biyu dake kasar da hannu cikin hari, sakamakon alakar dake tsakaninsu da ISIS.

Gwamnatin Sri Lanka ta bayyana cewa akalla yan kunar bakin wake ne suka kai harin a coci uku da otal uku, harin daya kashe akalla mutane dari uku da ashirin da daya, tare da jikkata wasu daruruwa, fiye da mutane dari hudu.

Zuwa yanzu gwamnatin ta kama mutane 40, da take zargin suna da hannu a harin, daga cikinsu har da wani dan kasar Syria. Amma wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnatin kasar Amurka ta tsegumta ma gwamnatin Sri Lanka bayanan sirri game da yiwuwar harin, amma tayi biris dasu.

Shima shugaban kasar Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe ya bayyana cewa akwai alamu dake nuna alaka tsakanin yan ta’addan da suka kai harin da kungiyar ISIS, yana ganin harin na da nasaba ga ramuwar gayyan harin da aka kai ma Masallata a New Zealand, don haka yace zasu sanya idanu akan yan ta’addan ISIS da suka koma Sri Lanka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel