Buhari ya ki maida hankali a kan ilmi amma Iyalin sa za su bude Jami’a – ASUU

Buhari ya ki maida hankali a kan ilmi amma Iyalin sa za su bude Jami’a – ASUU

Kungiyar ASUU ta Malaman jami’o’in Najeriya, tayi kaca-kaca da gwamnatin tarayya bayan jin labarin cewa Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari tana da niyyar bude jami’a da sunansa.

ASUU tayi Allah-wadai da wannan shiri na Hajiya Aisha Buhari, inda tace ba karamar katabora ba ce hakan. Kungiyar tace wannan yunkuri na Mai dakin shugaban kasar ya bayyana abin da ya sa ilmi yake kuka a Najeriya.

Malaman jami’ar sun bayyana cewa jawabin Aisha Muhammadu Buhari na kwanan nan, ya tabbatar da babban dalilin da ya sa gwamnatin shugaba Buhari ta ke rage kason harkar ilmi a kasafin kudin Najeriya tun 2016.

Shugaban ASUU na reshen Jami’ar Ibadan watau Deji Omole da kuma wani Ma’ajin kungiyar Farfesa Ademola Aremu, su ne su ka soki wannan shiri na Matar shugaban kasar a wata ganawa da su kayi da manema labarai jiya.

KU KARANTA: Sabon Gwamnan Adamawa zai karawa Malamai albashi

Buhari ya ki maida hankali a kan ilmi amma Iyalin sa za su bude Jami’a – ASUU
Aisha Buhari tana so ta kafa Jami'ar Muhammadu Buhari
Asali: UGC

Omole yake cewa ya kamata yanazu jama’a su san cewa ba gyaran harkar ilmin Boko bane a gaban wannan gwamnati inda yanzu Iyalin shugaban kasar ke neman yadda za ta kafa jami’a mai zaman kan-ta da hakin kan kasashen waje.

Daily Trust ta rahoto wannan ne a Ranar Talata 23 ga Watan Afrilu inda wadannan jiga-jigan ASUU na reshen jami’ar Ibadan su ka soki lamirin Uwargidar shugaban kasar a mabanbantan hirar da su kayi da ‘yan jarida a kwanan nan.

Idan ba ku manta ba, wajen wani taro da aka yi a garin Yola da ke cikin jihar Adamawa Ranar Asabar dinnan da ta gabata, Matar shugaban kasa Buhari tace tana son bude jami’a da sunan Mijinta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng