Gwamnatin Fintiri za ta biya Malamai fiye da N30, 000 – Kungiyar NUT

Gwamnatin Fintiri za ta biya Malamai fiye da N30, 000 – Kungiyar NUT

Mun samu labari cewa kungiyar NUT ta Malaman Najeriya da ke jihar Adamawa, ta na sa rai cewa gwamnatin PDP da za a kafa kwanan nan a jihar za ta karawa Malaman makarantan jihar albashi.

Shugaban kungiyar ta NUT ta bayyana cewa sun gamsu lallai sabon gwamnatin Ahmadu Umaru Fintiri za ta biya malaman da ke koyarwa a makarantun gwamnatin jihar Adamawa kudi N32, 000 a matsayin albashin na kowane wata.

Rodney Nathan, wanda yake jagorantar kungiyar ta NUT ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, na rattaba hannu a kudirin karin albashi a Najeriya, inda yanzu kowane ma’aikaci zai rika samun akalla N30, 000 duk wata.

Nathan yace Malaman jihar na sa rai a rika biyan su N32, 000 ne a maimakon N30, 000 din aka sanya ya zama mafi karancin abin da ma’aikata za su rika dauka. Kungiyar ta nemi Malamai su marawa gwamnatin Fintiri mai-zuwa baya.

KU KARANTA: Kashi 95% na Gwamnoni ba su da karfin kara albashi – Umahi

Gwamnatin Fintiri za ta biya Malamai fiye da N30, 000 – Kungiyar NUT
Umaru Fintiri yayi wa Malamai alkawarin N32, 000 a Adamawa
Asali: UGC

Nathan yace wannan sabon karin albashi yana cikin alkawarin da Fintiri ya dauka a lokacin yana takarar neman gwamnan jihar a zaben da ya gabata. NUT tace tana da yakinin cewa sabon gwamnan ba zai saba wannan alkawari ba.

NUT ta kuma yi kira ga Umaru Fintiri da ya duba matsalolin da harkar ilmi yake fuskanta a jihar Adamawa irin su matsalar sakin alawus da kudin Malamai, da kuma rashin karin girma da Malaman jihar Adamawa ke fuskanta.

Haka zalika wannan kungiya ta Malaman makaranta ta bayyana cewa karin albashin da za ayi, zai taimakawa duk ma’aikatan da ke kasar, tare da kira ga Malaman da su kara kwazo a na su bangaren.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng